Sabon gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tofa albarkacin bakinsa kan abin da ya faru tsakaninsa da uwargidan shugaban hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Magaji Bichi, jim kadan gabanin zaben 2023.
Gwamna Yusuf ya ce matar Bichi ta yi barazanar hana shi zama gwamnan jihar Kano a zaben 2023.
- An Bayyana Ranar Buga El Clasico Tsakanin Real Madrid Da Barcelona
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Wani Sabon Hari A Kogi
Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Talata a lokacin da yake tattaunawa da malaman Addinin Musulunci a gidan gwamnati da ke Kano, domin neman goyon bayan gwamnatinsa.
Idan dai za a iya tunawa a wani lokaci gabanin zaben, an yi ta cece-kuce a kafafen sada zumunta kan rikicin da ya barke tsakanin magoya bayan Yusuf, a lokacin da uwargidan shugaban DSS a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
Gwamnan, koka kan yadda wasu malaman Addinin Musulunci suka je gidajen rediyo suna zarginsa ba tare da sanin hakikanin abin da ya faru tsakaninsa da Misis Bichi ba.
“Bayan jami’an DSS sun ci mutuncin mutanenmu, sai na gana da ita na kai korafi, sai ta fara zagina, ta ce na rantse ba za mu taba bari ka zama gwamnan jihar Kano ba.”
Gwamnan ya kuma yi zargin cewa uwargidan shugaban DSS din, daga bisani ta hana shi shiga jirgin kasuwanci bayan da ya biya kudin tikitin tikitinsa, inda ya kara da cewa wasu malaman Kano ma sun yi ta sukarsa duk da cewa shi aka cutar ba tare da jin nasa bangaren ba.
Don haka Yusuf ya shaida wa malaman da suka halarci taron cewa zai mutunta dukkan malaman Addini a jihar, amma ya yi gargadin cewa ba zai lamunci da masu sukar gwamnatinsa ba a cikinsu.