Hukumar jin dadin Alhazai ta Kasa NAHCON, ta lashi takobin kawo karshen takaddamar da ake yi na yiwuwar wasu maniyyata aikin Hajji da ake ganin hukumar ka iya barin su a Nijeriya bayan sun kammala biyan kudadensu na aikin Hajji, duba da yadda lokacin fara aikin Hajjin ke kara gabatowa, tare da sanin dokar kasar Saudiyya ta rufe dukkanin filayen tashi da saukar jiragen samanta yayin da wa’adin hakan ya cika.
Kwamishina na PRSILS, Sheikh Sueiman Momoh, shi ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya kira a babbar Shalkwatar hukumar dake Abuja a ranar Talata, inda ya ce, a halin yanzu mahajjatanmu na Nijeriya wadanda Saudi Arebiya ta amince mana 95,000, to a yau mun kwashe mahajjata 67,000 suna tsakanin Madina da Makka, mafi yawa dai suna cikin Makka, abin dai ya rage mana a cikin 95 da za mu kammala kwashewa shi ne 6000, wadannan mutum dubu shidan suma muna ba da tabbacin babu wanda zai saura a Nijeriya sai mun kwashe su nan da kankanin lokaci, babu wani maniyyaci da muka yi wa Biza da zai yi saura a Nijeriya sai ya sauke farali in sha Allahu.
Sannan akwai ‘yan jirgin yawo suma za mu kammala kwashe su cikin wannan lokaci insha Allahu.
” Wadancan 67,000 da muka riga muka kai su kasa mai tsarki, an kammala dukkan abin da ya kamata a kammala na duk irin abubuwan da ya kamata a ce mahajjaci ya samu domin ya ji dadin gudanar da aikin Hajjinsa cikin kwanciyar hankali, da suka hada da ingantattun masaukai, motocin zirga-zirga, kula da lafiya da dukkan abin da ya dace a tanada gaba daya daga Makkan har Madinan mahajjatanmu ba su da matsala, wajen kula da lafiyarsu mun yi kyakkyawan shiri kan haka domin su samu nutsuwa, domin mahajjaci yana bukatar nutsuwa domin ya je ibada ne.
“Akwai wani tsari da muka gabatar na yadda Alhaji zai saurin fahimtar masaukinsa koda ya tsinci kansa cikin dimuwa, akwai kuma jami’ai da muka tanada domin yin hakan, ya zuwa yanzu ba mu da wata damuwa ko wani kokwanto akan Alhazanmu mun yi kyakkyawan shiri,” in ji shi.
Kuma wannan samun gurbi na adadin mutanen da na ya samu ne saboda kyakkyawar nasara da abin yabawa da muka samu daga kasar Saudiya. Kuma kafin ranar 24 ga watan nan da muke ciki, wato ranar da Saudiya za ta rufe shiga dukkan maniyyatanmu da suke kasa za mu kwashe su da yardar Allah kamar yadda na ambata.
Shi ma da yake amsa tambaya ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron na ‘yan jarida akan karafe-karafen da ake samu na cewar ana barin wasu mahajjatan a kasa, Daraktan Gudanarwa da Kula da Ma’aikata na Hukumar Dakta Ibrahim Sodangi, ya ce ”
Kowane aikin Hajji yana zuwa da tasa larurar, misalin Hajjin da ya gabata bamu samu guraben tafiyar maniyyata a cikin lokaci ba har sai da ya kai ga azumi ya wuce da kusan wata daya sannan suka ba da sanarwar za a yi aikin Hajji, Alhamdu lillahi shi ya sa muka sa masa suna Hajjin gaggawa, an yi an gama lafiya.
“A wannan karon ba na jin za samu matsalar barin Alhazai koda yake akwai wasu jirage wanda daya biyu sun dan samu matsala na rashin samun abin da muke kira gurbi, akwa kuma wasu dalilai da za mu iya cewa daga gare mu ne, kuma mafi yawa daga Saudi Arebiya ne, daga garemu din wani lokaci za ka ga jirgi ya zo su hukumar Alhazai na jihohi ko basu samu abin da ake kira BTA ba ko basu samu Yelloe Card ba da dai ire-irensu, amma wannan karon cikin yardar Allah ba mu samu wannan korafe-korafen da yawa ba.
” An zo kuma an sake samun matsalar Biza, wannan matsala ta samu ne tsakanimu da kudaden da muka tura, sani cewa duk wasu ayyuka na aikin Hajji ba da Naira ake yi ba da Dala ake yi, daga nan CBN zai tura mana kudaden da muke so za mu yi amfani da su a saudiya, Dala za ta canja zuwa asusunmu a Saudi Arebiya. Duk da jinkirin samun Bizar a yanzu haka mun kwashi maniyyatanmu kusan kashi 90, sauran ragowar za mu kwashe su in Allah ya so kafin zuwa ranar da Saudiya za su rufe shiga wato 24 ga wannan watan, abin ma ba zai kai wannan lokacin ba, in ji shi.
Da aka tambaye shi kan batun ‘yan adashin gata da aka ce an samu tangarda kuwa, sai ya ce ” Kamar yadda muke fadi muna kiran Allah ne, tangardar da aka samu na ‘yan adashen gat aba daga ko ina ne ya yi muni ba sai daga Jihar Kaduna, abin da ya faru, Hukumar Alhazai ta kasa da ta jihohi mun zauna an yi yarjejeniya, kashi 60 shi ne ake ba Alhazai na Kibogi, kashi 40 kuma shin w wanda ake ba wa ‘yan adashin gata, yarjejeniya an yi kuma kwai ta a rubuta kuma an sanar da kowa ya sani Jihar Kaduna an basu adadin Alhazansu, ba zan iya fayyace adadin duka ba amma na sani in aka lissafa za a ga 6000 ne da darurruka wanda kuma har da wadannan ‘yan adashin gatan, in kuma ka yi lissafin 6000 nan in ka cire kashi 40 za ka samu kusan 2000, to ka ga 2000 nan ‘yan adashin gata ne ya kamata a ba wa.
Sannan akwai lokacin da aka ba da wa’adin cewa kowace jiha ta turo kudaden da ta karba a wurin maniyyatanta, wannan adadi ya kai wadansu jihohin basu biya kudaden guraben da aka biya su ba, ire-iren wadannan akan rage musu kujeru, to da sauran ire-irensu.