Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya ce, kwamitin da Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC) ta kafa da aka dora wa alhalin bayar da shawarorin hanyoyin da za a bi wajen raba wa al’ummar kasa tallafi da gudunmawa sakamakon radadin cire tallafin Mai da ake fuskanta, za su gudanar da aikinsu tukuru domin muradin ‘yan kasa baki daya.
Gwamna Bala wanda ke wakiltar shiyyar Arewa Maso Gabas a cikin kwamitin ya shaida hakan ne a lokacin da ke ganawa da ‘yan jarida a Bauchi.
A cewarsa, mambohin kwamitin wadanda suke karkashin jagorancin gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Nasiru Idris, za su tabbatar dukkanin ‘yan kasa sun samu tallafi a kowani bangare domin rage musu radadi halin da aka tsinci kai sakamakon cire tallafin Mai ba tare da la’akari da banbancin jam’iyyar ba.
Ya ce, “Dukka da Gwamnonin da suke bangaren adawa da na gwamnati mai ci ta APC sun fahimci yunkurin da gwamnatin tarayya ta dauka bisa dacewa, don haka akwai tabbacin ba za a siyasantar da yunkurin ba.”
A cewarsa, NEC da wakilan kungiyoyin kwadago sun fahimci alfanu da kalubalen da ke tattare da cire tallafin Mai, da hakan ya janyo wa al’ummar kasa musamman talakawa shiga matsatsi da kuncin rayuwa, don haka da bukatar a samar da tallafi mai ma’ana domin rage radadin.
Kan hanyoyin da ke da bukatar agajin gaggawa kuwa, Gwamma Bala Muhammad, ya ce kwamitin zai ba da shawarar karin albashi ga ma’aikata da kuma samar da tallafi ga al’ummar kasa, samar da motocin bas-bas domin rage wa jama’a wahalar sufuri da kawo shirye-shiryen masu fa’ida da al’ummar za su amfana.
Ya ce, kwamitin za su gabatar da rahoton su nan da sati biyu ga Majalisar Tattalin Arzikin Kasa domin daukar matakai na gaba.
Ya nemi al’ummar kasa da su kara hakuri kan halin da suke ciki, da fatan Gwamnatin tarayya za ta tabbatar da yin amfani da shawarorin da za su bayar domin rage wa jama’a wahala da radadi.