Kamar yadda aka sane, tun bayan zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, wasu jam’iyyu da ‘yan takaransu sun kalubalanci nasarar Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin shugaban kasa a kotun sauraron kararrakin zabe.
A makon jiya ne dai Shugaba Tinubu ya shigar da bukata a gaban kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ke rokon a yi watsi da korafin jam’iyyar APM.
Kotun sauraron kararakin zaben shugaban kasa mai alkalai biyar karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Tsammani, ta ki amince da bukatar domin bai wa jam’iyyar cikakken kofar samun adalci yadda ya dace.
Jam’iyyar APM da dan takararta, Chichi Ajei, sun shigar da korafi gaban kotun ne da suke zargin cewa Tinubu bai cancanci shiga a dama da shi a zaben shugaban kasan ba bisa zargin yankan fom har guda biyu da abokin takararsa Kashim Shettima ya yi.
Lauyan da ke jagorantar tawagar lauyoyin Tinubu, Wole Olanipekun (SAN), ya buga misali da cewa, kotun koli a ranar 26 ga watan Mayu ta yi fatali da wani kara makamancin wannan da jam’iyyar PDP ta shigar bisa rashin madafa da manufa.
Kazalika, wasu jami’an hukumar zabe su uku sun shaida wa kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa yadda aka kasa shigar da sakamakon zaben kai-tsaye zuwa na’urar da aka ware don yin hakan a kan lokacin da aka tsara a yayin zaben shugaban kasa da ya gudana.
Shaidun su uku masu suna Janet Nuhu Turaki, Christppher Bulus da kuma Bictoria Sani wadanda suka yi wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) aiki a matsayin ‘Presiding Officers’ a Jihohin Bauchi, Yobe da Katsina.
Lauyan jam’iyyar PDP, Eyitayo Jegede (SAN) da Atiku Abubakar ne ya gabatar da shaidun a ranar Litinin da ta gabata, Janet Nuhu Turaki ta tabbatar da cewa aikin zabe ya tafi cikin nutsu da kwanciyar hankali kamar yadda aka tsara har zuwa lokacin shigar da sakamakon a cikin na’urar a yayin da aka samu matsalar rashin turawa kai-tsaye.
Ta kuma shaida wa kotun cewa sakamakon zaben da aka amsa ta cikin fom daga wakilan jam’iyyu da ita kanta a matsayin babbar jami’ar INEC a inda ta jagoranci zaben duk sun sanya hannu a takardar.
Christopher Bulus ita kuma cewa ta yi sakamakon zaben sanatoci da ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a rana daya da na shugaban kasan bai samu matsalar aikewa da sakamako ka-tsaye ba, illa na shugaban kasa aka samu matsalar rashin tafiyar sakamakon kai-tsaye zuwa ga na’ura.
Ita ma dayan shaidar, Sani ta ce ba za ta iya tuna dan takarar da ya ci zaben shugaban kasa a Jihar Katsina ba, sai dai ta ce a karshe dai ba a kammala zaben cikin dadi yadda aka so ba domin sakamakon bai shiga cikin na’urar da aka tsara kai-tsaye ba.
Sai dai shafin yanar gizo ta Amazon Web Serbice (AWS) wanda ya bayyana a gaban kotu a matsayin shaidar jam’iyyar LP da dan takararta, Peter Obi, ya shaida wa kotun cewa shafukansu ba su gamu da wata matsalar fasaha ba a lokacin zaben shugaban kasan da aka yi ranar 25 ga Fabrairu.
Hukumar INEC ta kare kanta daga korafin LP da Obi da ke cewa akwai kura-kuran fasaha da aka samu a http 500 a lokacin zaben shugaban kasan.
Injiniyar kamfanin Amazon, Clarita Ogar, ta shaida cewar shafinsu bai samu ko tangarda ba a lokacin zaben shugaban kasan.
Ko da yake, Lauyan INEC, Abubakar Mahmoud (SAN) da na Tinubu, Wole Olanipekun (SAN), da na APC, Charles Edomsomwan (SAN) dukkaninsu sun yi watsi da shaidar nata da cewa ka da a amince da shi.
A wani babin, Lauyoyin jam’iyyar LP, Liby Uzoukwu (SAN), da Jibrin Okutepa (SAN) sun yi korafin cewa INEC ta kasa ba su kayayyakin da suka nemi da kuma gasa amsa korafinsu yadda ya dace.
Sun ce, suna da sauran mako daya ne kawai su kammala da korafinsu amma INEC tana kawo musu tsaiko da matsala a kokarinsu na samun muhimman kayayyakin da aka yi amfani da su a lokacin zabe.
Okutepa ya ce rahotonnin na’ura da aka sanya hannu a ranar 29 ga watan Mayu an bayar ne kawai a ranar Litinin da wasu ‘yan kalilan na kananan hukumomin Legas da Gombe.
Sai dai kuma Lauyan INEC, Mahmoud SAN, ya ce sun samu takardar sammaci kan batun shaidu ne kawai ba ga INEC ba, ya kuma kara da cewa lauyoyin LP kila ba su bin matakan da suka kamata.
Bayan muhawarar lauyoyin, jagoran alkalan, ya bukaci lauyoyin da su ba da hadin kai don yi abun da ya kamata, yana mai cewa kotun tana da muradin wanzar da adalci da kare martabar kasa.
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa a zaman da kotun da ya gudana a ranar Talatar da ta gabata, jam’iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar sun rage shaidunsu zuwa 30 kuma za su rufe kararsu a ranar Alhamis kan korafin da suke yi na kalubalantar nasarar Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Masu korafin, kamar yadda yake a rahoton sharan fage na sauraron karar ya kamata su rufe karar tasu ne a ranar Talata, amma jagoran lauyoyinsu, Chief Chris Uche (SAN) ya shaida wa kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa cewa sun rasa kwana biyu cikin ranakun da aka ware musu don haka ne ya nemi a sake dawo musu da kwanakinsu biyu.
Atiku da PDP, sun shaida wa kotun a lokacin sharan fagen sauraron karar, cewa za su gabatar da shaidu har 100 da za su tabbatar da korafin da suke yi, sai dai har zuwa ranar Talatar da ta gabata, shaidu 25 ne kawai suka iya gabatarwa.
Da yake zantawa da ‘yan jarida, jagoran lauyan masu kara, Uche SAN, ya ce da yiyuwar za su sake kiran shaidu guda 5 da hakan zai ba su damar gabatar da shaidu har guda 30 a kan korafinsu na neman a kwace kujerar shugaban kasa daga hannun Tinubu a dawo musu da ita.
Tun da farko, masu korafin sun nuna yadda suka sha wuya kafin suka samu asalin kwafi na bayanai daga CTC a hannun hukumar zabe da hakan zai taimaka musu wajen nuna kura-kuran da aka tafka a zaben.
A gaban kotun, lauyoyin Atiku da na PDP sun shaida wa kotun cewa samun kwafin kayan aikin daga wajen INEC ya ba su matukar wuya sai da ya zama tamkar neman makami daga wajen abokin karawa, amma duk da hakan sun yaba wa jagoran tawagar lauyoyin INEC, Abubakar Mahmoud (SAN) bisa taimaka musu wajen samun bayanan daga INEC.
A bari guda, lauyan INEC, Kemi Pinhero (SAN) ya shaida wa kotun cewa jami’an INEC sun kawo bayanan ne daga dukkanin sassan kasar nan amma har yanzu masu korafin ba su biya satifiket na bayanan ba.