Shugaban Kasa, Bola Tinubu, ya bada labarin yadda wani Sojan ruwa ya sharara masa mari bisa tsula masa kudin fasinja fiye da yadda ake amsa ba da gangan ba a lokacin da yake direban Tasi a kasar Amurka.Â
Wannan na kunshe ne cikin labarin yadda ya taso da rayuwarsa da aka wallafa a bayan manyan jaridun Nijeriya.
Tarihin rayuwar da aka masa take da ‘Tinubu: rayuwata a matsayin direban Taksi a Amurka’, da fitaccen dan jarida, Mike Awoyinfa, ya wallafa.
A cikin tarihin rayuwar Tinubun, ya ce, ya yi aiki a matsayin direban Taksin da baida lasisi a garin Chicago da ke Amurka inda ke aikin jigilar kwaso fasinjoji daga filin jirgin sama zuwa inda za su sauka.
Shugaban kasan ya ce ya kama sana’ar tuki ne da nufin samun kudin da zai rayu kafin ya tafi makaranta.
Ya nakalto, “Mun samu mota (da aka taba amfani da ita) da ba ta da rijista da ake kira Gypsy, wacce muke shiga da sunan kabu-kabu ‘taksi’. Muna kwasan fasinjoji daga filin jirgi mu kai su wurare amma ba ko’ina ba, kamar otel-otel saboda ba ko’ina ne motar da ba ta da lasisi ba za ta shiga.
“Muna yin hakan ne na ‘yan lokuta domin mu samu wasu ‘yan kudade. Bolaji ya tafi zuwa Tennessee, ni kuma na zarce zuwa Chicago.
“Ya kamata na fara zuwa makaranta a watan Afrilu. Amma na jingine har zuwa watan Satumba saboda na tara kudi. Zuwata Chicago ke da wuya, kai tsaye na wuce zuwa Kwalejin Richard Daley. Gwanin ban sha’awa.
“Na samu zarafin biyan kudin dakina da na kudin makaranta a jami’ar Chicago.”
Ya cigaba da bayanin yadda ta kaya da yadda wani Sojan ruwa ya taba marinsa a fuska saboda ya cajeshi kudin taksi da ya wuce inda ake amsa bisa kaisa wani wuri da ke kusa-kusa.
“A matsayina na direba, akwai wani abun da ba zan taba mancewa da shi ba, wani lokaci na fadi kudin Taksi ga wani Sojan ruwa da ya dawo cikin kasar fiye da adadin da ake karba na masa ‘tsada kenan’. Kuma ba da gangan na masa ba,” Tinubu ya bayyana.
“A zahirin gaskiya ni ban san wajen ba. Kuma babu wani dan GPRS a wadannan kwanakin balle wani ya kwatanta min wajen. Don haka, shi sojan shi ne ya kwatanta inda gidan nasa yake a wani unguwa a Virginia.
“Da na fada masa farashin kudin da zai biyani kwatsam amsar da zai ba ni shi ne sharara min mari a fuskata. Ya ce ya kamata na san hakikanin farashin zuwa wurin da ya fada min. Ya mareni ya ba ni kudin kuma.”