Dan wasa mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Edouard Mendy ya koma kungiyar Al-Ahli da ke Kasar Saudiyya, a ranar Laraba, ya zama dan wasa na uku da ya bar Chelsea zuwa Saudiyya a karshen kakar wasa ta bana.
Mendy dan kasar Senegal, an bayar da rahoton cewa, an sayar da shi ne ga Al-Ahli a kudi kusan fam miliyan 16 (dala miliyan 20) bayan da ya rasa gurbinsa ga Kepa Arrizabalaga a rabin kakar wasannin bara na wa’adin karshe.
“Maraba da Mendy… mafi kyawun masu tsaron raga na duniya,” Al-Ahli ta wallafa a shafukan sada zumuntanta tare da faifan bidiyo na dan wasan mai shekaru 31 yana sanya hannu kan kwantiraginsa.
Mendy ya taimaka wa Chelsea ta lashe gasar zakarun Turai a 2021, amma sau daya kawai ya buga wa kungiyar wasa bayan ya dawo daga gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a bara.