Yau Alhamis 29 ga wata ne, aka kaddamar da bikin baje-kolin tattalin arziki da cinikayya na kasashen Sin da Afirka karo na uku a birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin, wato China-Africa Economic and Trade EXPO. Ana sa ran cewa, bikin na bana zai kara taka muhimmiyar rawa, da baje karin hajojin Sin da Afirka, al’amarin da zai sanya sabon kuzari ga hadin-gwiwar bangarorin biyu.
Yawan kamfanonin cikin gida da waje da suke halartar bikin na bana, ya kai 1500, adadin da ya karu da kaso 70 bisa dari idan aka kwatanta da bikin da ya gabata. Kana, kayayyaki 1590 daga kasashe 29 ne, aka yi rajistar shigar da su baje-koli na bana. Ana kuma shirin rattaba hannu ko kuma gudanar da shawarwari kan wasu ayyukan hadin-gwiwa guda 218, wadanda jimillar darajarsu ta kai dala biliyan 19.1.
A bana ne ake cika shekaru 10 da gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kasar Sin ta yi, kana shekaru 10 da kasar ta fitar da muhimman manufofinta kan nahiyar Afirka, wato nuna “Sahihanci”, da “Sakamako na hakika”, da “Dangantakar abokantaka”, da kuma “Aminci”. A cikin wadannan shekaru 10, kwalliya ta biya kudin sabulu, wajen karfafa hadin-gwiwar Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da kasuwanci.
Bikin baje-kolin tattalin arziki da cinikayyar Sin da Afirka, dandalin hadin-gwiwa ne mafi girma a karkashin tsarin FOCAC, wato dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka. Tun daga shekara ta 2019, a kan shirya irin wannan biki bayan kowane shekaru biyu-biyu. A ranar 2 ga watan Yuli ne, za a kammala bikin na bana.
Sannan, a yau Alhamis, babbar hukumar kwastan ta kasar Sin ta gabatar da alkaluman cinikayya tsakanin Sin da Afrika karon farko yayin bikin baje kolin harkokin cinikayya na Sin da Afrika karo na 3. Bisa alkaluman, makin cinikayya a shekarar 2000 ya kai 100, yayin da a shekarar 2022 ya karu zuwa maki 990.55, abin da ya bayyana saurin bunkasuwar cinikayyar bangarorin biyu. A cikin wadannan shekaru kuma, yawan kudin dake shafar cinikin kayayyakin da Sin ke fitarwa zuwa Afrika ya ninka fiye da sau 20, wanda ya karu da kashi 17.7 a ko wace shekara. Hakan ya sa Sin ta kai matsayin koli a fannin ciniki da Afrika a cikin shekaru 14 a jere.
A wannan rana kuma, an bude dandalin hadin kai a fannin kiwo lafiyar bil Adama da tsirrai tsakanin Sin da Afrika wato SPS a birnin Changsha, hedkwatar lardin Hunan. Yayin dandalin, wakilin babbar hukumar kwastan ya yi bayani kan nagartattun matakai da za su tabbatar da kafa hanyar samar da rangwame ga kayayyakin aikin gona da Sin za ta shigo da su daga Afrika. (Murtala Zhang, Amina Xu)