Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya sanya hannu kan dokar da ‘yan majalisar dokokin jihar ta yi na kisa ga wanda aka kama da hannu cikin ‘yan fashin daji, masu garkuwa da mutane da masu kai wa ‘yan bindiga rahoto.
Matawalle, ya sanya wa dokar hannu ne a ranar Talata bayan da shugaban majalisar dokokin jihar, Muazu Magarya, ya gabatar masa da dokar a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.
- Alaramma Sadeeq Umar Da Ya Wakilci Nijeriya A Musabakar Al-qur’ani Ta Tanzaniya Ya Rasu
- ‘Yan Bindiga Sun Sace DPO A Kaduna
LEADERSHIP Hausa ta nakalto cewa, dokar ta tanadar da daurin rai da rai ga masu satar shanu, kuma za a kafa akwati na amsar koke daga jama’a a gaban gidan gwamnatin don kokarin nemo hanyoyin samun nasarar kawo karshen ayyukan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a fadin jihar.
A jawabinsa, gwamnan Jihar Bello Matawalle, ya bukaci al’ummar jihar da a kowane lokaci suke amfani da akwatin wajen bada dukkanin bayanan sirri domin ganin an dauki matakan da suka dace wajen magance matsalolin ‘yan fashin daji.
Shugaban .ajalisar dokokin jihar, Muazu Magarya, ya bayyana cewa, sun yi wadannan dokokin ne dan samar wa al’ummar jihar Zamfara mafita mai dorewa.
Ya gode wa gwamnan bisa sanya hannu kan dokar tare da fatan jami’an jihar za su bada gudunmawarsu wajen tabbatar da wannan nasarar da aka sanya a gaba na kawo karshen ‘yan ta’adda a jihar.