• English
  • Business News
Monday, July 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amfanin Juna Shi Ne Tushen Hadin Gwiwar Afirka Da Sin

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Amfanin Juna Shi Ne Tushen Hadin Gwiwar Afirka Da Sin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Kowa na cewa yanayin tattalin arzikin duniya ba shi da kyau yanzu, amma idan ka halarci taron baje kolin tattalin arziki da ciniki na Sin da Afirka, da ya gudana a birnin Changsha na kasar Sin a kwanakin baya, to, za ka ce kamar maganar ba ta yi daidai ba.

Saboda duk wani mutum da ya halarci taron ya ji mamakin yadda yanayin bikin ke da armashi, inda ake samun cunkuson mutane matuka. Alkaluman da aka gabatar bayan rufe taron baje kolin a jiya sun nuna cewa, cikin wa’adin taron na kwanaki 4, an nuna nau’ikan kayayyaki kimanin 1600 na wasu kasashe 29 dake nahiyar Afirka, inda aka samu mutane fiye da dubu 100 da suka halarci taron baje kolin, tare da kulla yarjeniyoyi 120, wadanda darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 10.3.

  • Kasar Sin Ta Samu Ci Gaba A Fannin Raya Jiragen Masu Matukar Saurin Tafiya 

Abun da ya fi burge ni a wajen taron baje kolin na wannan karo, shi ne yadda aka nuna dimbin kayayyakin amfanin gonan kasashen Afirka, irinsu kifaye na kasar Madagascar, da man zaitun na kasar Aljeriya, da tattasai na kasar Malawi, da dai sauransu. Kana wani nau’in ganyen shayi mai launin jar galura na kasar Kenya ya samu karbuwa sosai, saboda yadda yake kunshe da sinadarai masu gina jiki. Inda aka sayar da ganyen na ton 2, a cikin ranar farko da aka gudanar da bikin.

Ban da amfanin gona, an samu damar nuna wasu kayayyaki masu daraja kirar kasashen Afirka, irinsu tufafi, da lemu iri-iri, da kayan kwalliya na shafe-shafe, da dai sauransu, don neman shigar da su cikin kasuwannin kasar Sin. Cikinsu har da jakunkuna da tufafi masu kyan gani da wani saurayi dan kasar Zambia mai suna Kabaso ya kirkiro, wadanda suke da salon musamman na Afirka. A cewarsa, ya halarci taron baje kolin ne don yin bincike kan yanayin kasuwannin Sin, don neman sayar da kayayyakinsa ga karin jama’ar kasar.

Cikin abubuwan da aka nuna a wajen taron baje kolin, har da dandali na ciniki. Inda wani shafin yanar gizo mai taken Kilimall yake taimakawa sayar da kayayyakin Sin zuwa kasashen Afirka, gami da shigar da kayayyakin kirar kasashen Afirka cikin kasar Sin. Zuwa yanzu shafin nan ya sayar da kayayyaki na kimanin nau’ika miliyan 1 ga mutane fiye da miliyan 10, inda ta samar da guraben aikin yi fiye da 5000 a kasar Kenya kacal.

Labarai Masu Nasaba

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

Sa’an nan ban da bikin baje koli, an gudanar da wasu bukukuwa kimanin 40 a gefen taron, tare da samar da sakamako mai gamsarwa. Misali, a wajen taron dandalin tattaunawar kasar Sin da kasashen Afirka ta fuskar kiwon lafiya da yin amfani da ganye wajen kare lafiyar jiki, bangarorin Sin da Afirka sun yi alkawarin daidaita ka’idojinsu na tantance ingancin kayayyaki a kwastam don magance yaduwar cutuka, ta yadda za a iya shigar da kayayyaki amfanin gonan kasashen Afirka cikin kasuwannin Sin cikin karin sauki. Kana a wajen wani taro na karfafa ciniki a fannin kayayyakin masana’antu, wani yankin masana’antu na lardin Hunan na kasar Sin ya kulla yarjejeniya tare da hukumar fitar da kayayyaki ta kasar Kodibwa, inda suka samar da shirin hadin gwiwa don raya masana’antu.

Sai dai, abin tambaya shi ne, me ya sa ake iya gudanar da bukukuwan masu alaka da hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da ciniki cikin wani yanayi mai armashi, duk da wani yanayin tabarbarewa da tattalin arzikin duniya ke ciki? A ganina, zan iya yin amfani da maganar wani jami’in asusun Bill & Melinda Gates na kasar Amurka, mai suna Obai Khalifa, da ya fada wa ‘yan jarida a gefen taron baje koli na wannan karo, wajen amsa tambayar. A cewarsa, ya amince da yadda kasar Sin take kula da kasashen Afirka, inda ba ta kallon kasashen a matsayin nauyin da aka danka mata. Maimakon haka, kasar Sin ta dauki kasashen Afirka a matsayin abokan hulda, wadanda ake iya zuba musu jari don samun damar ci gaban tattalin arziki. Kana abubuwan da ya gani a wajen bikin baje kolin na wannan karo sun sa shi fahimtar huldar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, iri na amfanin juna.

Bayan da kayayyakin kasashen Afirka suka shiga cikin kasuwannin kasar Sin, masu samar da su dake kasashen Afirka za su samu karin kudin shiga, yayin da Sinawa za su samu damar more wadannan kayayyaki. Kana a lokacin da kamfanonin kasar Sin ke gudanar da wasu ayyuka a kasashen Afirka, lamarin zai ciyar da tattalin arzikin kasashen Afirka gaba, gami da haifarwa kamfanonin da riba. Dalilin yadda ake tsayawa kan manufar daidai-wa-daida da amfanin juna, ya sa hadin gwiwar Sin da Afirka a fannin tattalin arziki da ciniki ke dinga samun ci gaba, inda ake ba da gudummuwa ga kokarin kawar da wani yanayi na rashin tabbas a duniyarmu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Matsalar Tsaro Kalubale Ne Ga Samar Da Abinci -Bafarawa

Next Post

Daidaiton Ƙasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Ci Gaban Ƙasashen Duniya

Related

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
Daga Birnin Sin

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

1 hour ago
Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
Daga Birnin Sin

Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

2 hours ago
An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden
Daga Birnin Sin

An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

3 hours ago
Sin Ta Samu Iska Mai Ni’ima Da Ruwa Mai Inganci A Rabin Farko Na Bana
Daga Birnin Sin

Sin Ta Samu Iska Mai Ni’ima Da Ruwa Mai Inganci A Rabin Farko Na Bana

4 hours ago
Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar

5 hours ago
Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021
Daga Birnin Sin

Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021

6 hours ago
Next Post
Daidaiton Ƙasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Ci Gaban Ƙasashen Duniya

Daidaiton Ƙasar Sin Na Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Ci Gaban Ƙasashen Duniya

LABARAI MASU NASABA

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025

July 28, 2025
Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

Ambaliyar Ruwa: Adadin Mutanen Da Suka Rasu Ya Ƙaru Zuwa 23 A Jihar Adamawa

July 28, 2025
Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa

July 28, 2025
Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci

Kotun Ta Ci Tarar Hukumar NYSC Kan Haramtawa ‘Yan Bautar Ƙasa Mata Sanya Siket Da Tauye Musu ‘Yanci

July 28, 2025
An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

July 28, 2025
Sin Ta Samu Iska Mai Ni’ima Da Ruwa Mai Inganci A Rabin Farko Na Bana

Sin Ta Samu Iska Mai Ni’ima Da Ruwa Mai Inganci A Rabin Farko Na Bana

July 28, 2025
Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar

Sin Za Ta Ba Da Tallafin Kula Da Yara A Fadin Kasar

July 28, 2025
Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

Tinubu Ya Karrama Mata ‘Yan Ƙwallon Nijeriya Da Lambar Girmamawa (OON), Dala Dubu 100 Da Gidaje

July 28, 2025
Gwamnatin Sakkwato Ta Ƙaddamar Da Sababbin Motoci 30, Don BunÆ™asa Sha’anin Sufuri A Jihar

Super Falcons Sun Iso Abuja ÆŠauke Da Kofin WAFCON

July 28, 2025
Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021

Ana Ci Gaba Da Habaka Karfin Kudin Kasar Sin Tun Daga Shekarar 2021

July 28, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.