Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya bayyana cewa yayin da wasu ma’aikatansa ke da gidaje a kasashen waje da suke amfani da su a matsayin gidajen hutu, ba shi da ko gida daya a waje.
Dan kasuwar ya kara ba da wasu shawarwari don samun nasara a matsayin mutum a fagen kasuwanci.
- Dalilin Da Ya Sa Nake Shiga Sha’anin Gwamnatin Kano -Kwankwaso
- Gwamnatin Sakkwato Ta Kafa Kwamitin Binciken Mukaman Karshe Na Tambuwal
A wata hira da ya yi da manema labarai da aka buga kwanan nan a shafin Instagram na Tonyelumelu foundation, Dangote ya ce, “Mutane da yawa har da kanana, ya kamata mu yi taka-tsantsan domin yana daya daga cikin manyan batutuwa. Ya kamata mu ’yan Afirka, mu yi hasashen kudin da muke kashewa.
“Da zarar ka fara kasuwanci kuma sana’ar ta fara kyau, maimakon ka ci gaba da saka hannun jari a cikin sana’ar, sai ka fara kashe kudi kana tunanin za a ci gaba da samun riba. Akwai abubuwa da yawa a cikin kasuwanci don haka kuna bukatar mayar da hankali sosai.”
Dan kasuwar ya ci gaba da ba da shawarar cewa kashe kudi wajen sayen kayan alatu na iya dagula lissafin kasuwanci.
Da yake ba da misali da kansa, Dangote ya bayyana cewa, “Abubuwan alatu – suma suna daukar lokacinku wanda ba zai sa ku mayat da hankali kan kasuwancinku ba. Ina nufin, ba ni da wani gida a ko ina; amma na san mutanen da suke yi min aiki, suna da gida a Landan. Amma ni ba zan iya hakan ba.”