An tsinci wani jariri dan wata bakwai mai suna Habibu yana barci goye a bayan mahaifiyarsa bayan awa 24, da wasu ‘yan bindiga suka kashe ta a kan babbar hanyar Pandogari zuwa Allawa da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja.
An ruwaito cewa, ‘yan bindigar su tare hanyar ne a ranar 27 ga watan Yunin 2023, inda suka bude wa motar da ke dauke da fasinjojin wuta.
- JAMB Ta Haramta Wa Dalibar Da Ta Yi Sakamakon Bogi Sake Zana Jarabawa
- ‘Yan Sa-Kai Sun Kashe Mutum 6 A Zamfara
A cewar rahoton, ‘yan bindigar sun hallaka fasinjojin shida ciki har da mahaifiyar jaririn da kuma wata daliba mai suna Hauwa Aliyu ‘yar aji biyu a makarantar sakandaren kimiyya ta mata ta Maryam Babangida da ke garin Minna.
Shugaban kungiyar matasa na Lakpma, Jibril Allawa, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce ‘yan kungiyar sintiri ne suka tsinci jaririn goye a bayan mahaifiyarsa yana barci a yayin da suka je inda abin ya auku domin kwaso gawarwakin fasinjojin.
Ya ce, wani mai suna Abubakar Ismail, dan shekara 16 da samu raunuka a kirjinsa ya gudu zuwa wani waje mai nisan gaske, dauke da harbin albarusan ‘yan bindigar, inda daga baya aka gano shi kuma aka kai shi asibiti.
A wani labarin kuwa jami’in Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a jihar Ondo, sun kubutar da wani jariri daga hatsrin mota ya rutsa da mahaifiyarsa a karamar hukumar Ayegunle-Oka da ke Akoko ta Kudu a jihar.
Mahaifiyarsa ta rasu ne a cikin mota kirar Hiace Toyota bas mai lamba BWR563YL.
Kwamandan shiyya na FRSC da ke a Ikare Akoko, Ropo Alabi, ya ce an ceto jaririn ne a ranar Lahadi, inda aka mika shi ga ‘yan uwan marigayiyar.