Alhazan jihar Kwara 272 da suka yi aikin hajjin bana a kasar Saudiyya sun dawo gida Nijeriya ranar Laraba.
Alhazan sun taso daga filin jirgin sama na Jeddah da misalin karfe 8:30 na yammacin ranar Talata, inda suka isa filin jiragen sama na Murtala Mohammed da ke Ikeja, Legas da tsakar daren ranar Talata, daga bisani kuma kamfanin jirgin Air Peace ya dauko su daga Legas zuwa Ilorin babban birnin jihar Kwara a ranar Laraba. Da karfe 9:53 na safe inda suka sauka a filin jirgin saman Ilorin.
- Hajji 2023: Rukunin Farko Na Alhazan Nijeriya Sun Baro Saudiyya Zuwa Nijeriya
- Hajjin 2023: Gobe Talata Za A Fara Jigilar Alhazan Nijeriya Zuwa Gida
Daga cikin alhazan da suka iso tare da sauran alhazan akwai babban limamin Ilorin, Sheikh Mohammed Salihu, tsohon sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Mamman Jibril da ko’odinetan shiyya na Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) na jihohin Kwara, Ondo da Ekiti. Alh Jibir Fijabi.
Wasu daga cikin mahajjatan da sun hada da babban limamin garin Ilorin, Sheik Mohammed Salihu, sun godewa Allah da ya ba su damar gudanar da aikin hajjin cikin nasara tare da tabbatar da dawowarsu Nijeriya lafiya.
Sun bayyana jin dadinsu da yadda mambobin hukumar alhazai ta jiha da tawagar gwamnati suka yi a kasa mai tsarki.