Wata babbar kotun shari’a da ke zamanta a Ganye a jihar Adamawa ta yankewa wani Direban Adaidaita Sahu, Nuhu Pius, hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari kan samunsa da laifin kisan kai.
An yankewa Pius hukuncin kisan gillar da aka yi wa Gabriel Solomon, biyo bayan wani hargitsi da ya kaure a wurin wani shayi da ke kauyen Trigali, karamar hukumar Ganye ta jihar.
- Yadda Aka Shafe Shekara 14 Ba A Biya Tsofaffin Ma’aikata Fansho Da Kudin Sallama A Adamawa Ba
- Yadda Fintiri Da Atiku Suka Gudanar Da Bikin Sallah A Adamawa
Alkalin kotun, Mai shari’a Maxwell Pukuma, ya ce kotun ta yanke hukunci tare da samun Puis da laifi kan “kisan kai”.
Da yake yanke hukuncin, Pukuma ya bayyana cewa hukuncin zai fara aiki ne daga ranar da ake ci gaba da tsare wanda ake tuhuma ba tare da zabin tara ba.
Wanda aka yankewa hukuncin, Nuhu ya gurfana a gaban kotu a ranar 14 ga Afrilu, 2022 inda ya ki amsa laifin da ake zarginsa da shi.