Daga yammacin ranar 5 zuwa safiyar ranar 6 ga wata, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya ziyarci birnin Suzhou na lardin Jiangsu. Xi Jinping ya isa cibiyar baje kolin yankin masana’antu na Suzhou, da kamfanin HYC na Suzhou, da titin tarihi da al’adu na Pingjiang, don fahimtar yadda ake ginawa, da raya manyan yankunan kimiyya da fasaha na zamani, da yadda masana’antu ke yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da kuma yadda ake kare birane masu dogon tarihi da al’adu da dai sauransu.
Bugu da kari, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin cimma burikan rundunar ’yantar da al’ummar kasar Sin ko PLA na cika shekaru 100 da kafuwa, da bude sabon babin gina rundunar reshen gabashin kasar, da ma shirin yaki na rundunar.
Xi, ya yi tsokacin ne a yau Alhamis, yayin da yake duba ayyukan hedkwatar rundunar ta PLA reshen gabashin kasar dake lardin Jiangsu. Yayin rangadin, ya tabbatar da muhimmiyar gudummawar da rundunar reshen gabashin kasar ke bayarwa tun bayan kafuwarta, a fannin kare ikon mulkin yankunan kasar Sin, da tsaron hakkokin kasar na ruwa, da ma tallafin ta ga hadin kan kasar. (Mai fassara: Bilkisu Xin, Saminu Alhassan)