• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Hadin Gwiwa Da Kasar Sin Na Ingiza Bunkasar Kasashen Afirka

by CMG Hausa
2 years ago
Sin

Yayin da kasar Sin tare da kasashen Afirka ke kara azamar cika alkawuran da suka yiwa juna, na bunkasa hadin gwiwa da cudanya ta bangarori da dama, masharhanta na cewa “Kwalliya tana biyan kudin sabulu”, inda tuni hadin gwiwar kasar Sin da kasashen na Afirka ya haifar da ci gaban tattalin arziki, da kyautatuwar zamantakewar al’ummun sassan biyu. Alal misali, mun ga yadda bikin baje kolin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Afirka karo na 3 da ya gabata, ya kara karfafa alakar cinikayya, da tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen Afirka, tare da kara tabbatar da matsayin kasar Sin, na kasancewar muhimmiyar abokiyar cudanyar kasashen na Afirka a wannan fanni.

Idan ba a manta ba, yayin baje kolin na bana, wakilai daga kasashen Afirka 53, da karin wasu hukumomin kasa da kasa da dama sun hallara, kuma adadin masu baje hajoji a bikin ya kai 1,500, adadin da ya karu da kaso 70 bisa dari kan na shekarar 2021. Albarkacin matakai daban daban da sassan biyu ke dauka na raya huldar cinikayya da kasuwanci, yanzu haka Sin ta kai matsayin abokiyar cinikayyar Afirka mafi girma, kuma kasa ta hudu a girman zuba jari a nahiyar.

  • SCO Ta Ba Da Sanarwar Hadin Gwiwa Game Da Tsaro, Da Sauye-sauye Na Zamani

Bisa huldodin da Sin da kasashen Afirka ke rayawa, tasirin Sin a fannin bunkasar tattalin arzikin kasashen Afirka ya wuce batun samar da ababen more rayuwa kadai, domin kuma ya kunshi karin sassan samar da ci gaba daban daban. Ciki har da gina yankunan raya tattalin arziki na musamman da Sin din ke daukar nauyi a kasashen nahiyar da dama, wanda hakan ke samar da karin damammaki na bunkasa fannin masana’antun Afirka, da kuma kara fadada guraben ayyukan yi.

A daya bangaren, su ma kasashen Afirka ba a bar su a baya ba, wajen bullo da tsare-tsaren bunkasa cinikayya, da zuba jari tsakaninsu da bangaren Sin. Ga misali, yayin taron baje kolin kasa da kasa karo na 47 da ya gudana a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzania a farkon makon nan, an kebe ranar Talata a matsayin ranar kasar Sin, tare da kebe rumfuna sama da 100 na baje hajojin kamfanonin kasar.

Wannan mataki dai ya kasance wata dama dake kara jaddada muhimmancin alakar cinikayya tsakanin Sin da Tanzania, da ma sauran kasashen Afirka, wadda a wannan karo ta baiwa masu yawon bude ido zarafin kara fahimtar wannan kasa mai ni’ima da karbar baki.

LABARAI MASU NASABA

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Manazarta da dama na ganin a halin da ake ciki, Sin da kasashen Afirka na kara fadada cudanya mai armashi ta fuskoki da dama, ta yadda hakan ke haifar da karin damammaki ga junan su, da habaka samar da ababen more rayuwar jama’a musamman a kasashen Afirka, da ingiza ci gaban masana’antu da musaya, matakin da ko shakka babu, na yin matukar tasiri ga ci gaban kasashen Afirka, a matsayin su na kasashe masu tasowa. (Saminu Alhassan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 
Daga Birnin Sin

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka
Daga Birnin Sin

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika
Daga Birnin Sin

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Next Post
Magudin Jarrabawar UTME: Okebukola Ya Shawarci Makarantu Da Su Rungumi Tsarin JAMB

Magudin Jarrabawar UTME: Okebukola Ya Shawarci Makarantu Da Su Rungumi Tsarin JAMB

LABARAI MASU NASABA

Sabbin Ministoci

Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai

November 5, 2025
Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE 

November 5, 2025
Majalisar Kano Na Shirin Zartar Da Dokar Gwajin Kwayoyin Jini, Kanjamau Da Cutar Hanta Kafin Aure

Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu 

November 5, 2025
Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

Sin Za Ta Gyara Matakan Haraji Kan Kayayyakin Da Ake Shigowa Da Su Daga Amurka

November 5, 2025
Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Sanata Barau Ya Tsaya Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

November 5, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.