An samu barkewar cutar Diphtheria da ta kashe yaro mai shekara hudu a garin Dei-Dei da ke babban birnin tarayya Abuja, wanda hakan ya sa hankalin mutane ya tashi musamman ma la’akari da yadda kwayar cutar take yaduwa tsakanin mutane.
Hukumar Babban Birnin Tarayya ta tabbatar da yaduwar cutar bayan da aka yi gwajin mutane takwas a dakin gwajin da ke Gaduwa da hukumar hana yaduwar cutar ta gudanar.
- Bukatar Dakatar Da Kara Kudin Wutar Lantarki A Nijeriya
- Kamfanin Meta Mamallakin Facebook Ya Yi Wa Twitter Kishiya
Diphtheria cuta ce da take farawa da zazzabi wanda yake saurin yaduwa ta hanyar tari da kuma hamma, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar.
 “Idan abin ya ta’azzara, kwayar cutar tana iya yin guba da take sa wani farin abu a bayan makogwaro wanda ke toshe hanyoyin da iska za ta shiga, abin da zai samar da matsala wajen shakar iska ko hadiya, da haka ne sai a fara tari mai zafi. Akwai wani sashe na wuya na iya kumburi saboda kwayar cutar ta yi sanadiyar ta kama wurin.
 “A hankali gubar na iya haduwa da jini wanda hakan na iya samar da matsala da lalata naman zuciya da za su iya shafar jijiya, koda da saboda karancin kwayar halitta ta jini da ke sa rauni saurin warkewa”.
Cutar ana yin maganinta ta hanyar amfani da magani da kuma na yin allurar Diphtheria.
Domin kauce wa kamuwa da cutar, babban sakataren kula da lafiya na Abuja, Yahaya Batsa, ya yi kira da mutane su je su yi allurar rigakafi, su yi nesa da shiga cikin jama’a da kuma daina zama wuraren da babu tsafta. Ya ba da shawarar a yi wa yara allurar rigakafi kamar yadda ya dace sau uku na allurar Pentabalent.
Hukumar lafiya ta duniya ta yi bayanin cewar a tabbatar da yin allurar rigakafin cutar Diphtheria ga yara da samari, saboda gujewar barkewar cutar.
Akwai allurar rigakafi ta da take bukatar ba kamar yadda ake yi ba sau uku, wanda hakan zai sa a samu damar yi wa yara da yawa allurar rigakafin da ya kamata saboda kariya daga kamuwa da cututtuka kamar su Diphtheria.
Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya yana sa ran hukumar lafiya ta duniya za ta assasa yin allurar rigakafi nan da wata uku masu zuwa ko rubi’in shekarar 2023.
Alkalumma da aka samu daga hukumar lafiya ta duniya sun nuna cewa an samu wadanda suka kamu da cutar Diptheria 557 a Nijeriya daga watan Afrilu na 2023, ya shafi jihohi 21 daga cikin 36 tare da babban birnin tarayya.
An sanar da cibiyar hana yaduwar cututtuka da maganisu ta kasa a watan Disamba 2022, dangane da barkewar cutar Diphtheria a jihohin Kano da Legas.
Daga ranar 14 ga watan Mayu zuwa 9 ga Afrilu 2022, an samu wadanda ake kyautata sun kamu da cutar guda 1439, amma daga karshe an samu 557 ko kashi 39 da aka tabbatar da sun kamu da mutuwar mutum 73 daga cikin wadanda suka kamu da cutar.
A Nijeriya an fara samun labarin barkewar cutar Diphtheria a shekarar 2011 da ta shafi wasu wurare a kauyukan Jihar Borno, sashen Arewa maso gabas.
Alamun kamuwa da cutar sun hada da zazzabi, majina ta rika zuba, ciwon mashako, tari, idanu su yi ja, kumburin wuya, sai samun matsalar yin numfashi. Cutar Diphtheria tana saurin yaduwa ta hanyar cudanya da wanda ya kamu da ita.
Domin tabbatar da an kauce wa yiyuwar kamuwa da cutar, an yi kira da mazauna babban burnin tarayya su tabbatar da an yi wa ‘ya’yansu alluran rigakafi sau uku na Pentabalent wato yadda aka amince da sharuddan alluran rigakafi na kasa.