Tsohon dan wasan Manchester City, Yaya Toure ya ce sai da ya ce wa tsohuwar kungiyarsa ta Manchester City ta dauko Sadio Mane daga Southampton lokacin yana kungiyar.
Dan wasan Senegal din ya ci kwallo 21 cikin wasanni 67 da ya buga a Premier a kungiyar Saints daga 2014 zuwa 2016 kafin Liberpool ta dauke shi kan kudi fan miliyan 43. Sai da ya zama daya daga cikin abun dogaro ga kungiyar liberpool wanda ya lashe gasar zakarun Turai a shekarar 2019 sannan kuma ya lashe gasar Premier a kakar wasa ta 2019 zuwa 2020.
- Abin Da Ya Sa A Daminar Da Ta Gabata Masara Ta Yi Tsada -Shugaba
- ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Yi Wa Jama’a Kutse A Asusun Banki
Toure ya kwashe shekara takwas a Manchester City daga kakar wasa ta shekara ta 2010 zuwa 2018, wanda yana cikin wadanda suka ci wa kungiyar gasar Premier ta farko da kuma FA.
Da yake magana da manema labarai, tsohon dan wasan na Ibory Coast ya ce lokacin da yake Manchester City yana Southampton, yana mutunta shi kwarai da gaske, kuma ya rika yi wa shugabannin kungiyar magana akan dauko shi amma hakan bai yiwu ba.
A watan Yunin shekara ta 2022 ne Mane ya koma Bayern Munich kan kudi fan miliyan 35 bayan ya ci kwallo 120 cikin wasa 269 da ya yi a Liberpool, sannan ya ci manyan kyautuka shida.
A watan Maris din shekara ta 2020 Mane ya bayar da tallafin fan 41,000 ga kwamitin kasarsa da yake yaki da cutar Korona sannan ya kuma bayar da kyautar rigar Liberpool 300 ga mutanen garinsu gabanin wasan karshe da kungiyar ta buga da Real Madrid wanda ta yi rashin nasara.