• English
  • Business News
Thursday, June 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Haɗin Gwiwar Sin Da Majalisar Ɗinkin Duniya Na Da Tasiri Ga Makomar Zaman Lafiyar Duniya

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
Haɗin Gwiwar Sin Da Majalisar Ɗinkin Duniya Na Da Tasiri Ga Makomar Zaman Lafiyar Duniya
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Ƙasar Sin a matsayinta na mamba a ƙungiyar ta duniya wato Majalisar Ɗinkin Duniya, ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen ba da shawararta na tabbatar da ra’ayin bangarori daban-daban na gaskiya, kuma tana son taƙaita rashin daidaiton tattalin arziki da zamantakewar al’umma da ke illa ga yankunan duniya. Inganta haɗin gwiwa tsakanin Sin da MDD wajen samun ci gaba mai ɗorewa, da sauyin yanayi, da kirkire-kirkire na zamani, da kare hakkin dan Adam, wani babban mataki ne na tabbatar da daidaito da dawwamar zaman lafiyar a duniya. 

Ƙasar Sin na ci gaba da ciyar da wakilcin yankin kudu na duniya gaba ta hanyar faɗaɗa shirinta na BRICS da shirinta na shawarar ziri ɗaya da hanya ɗaya (BRI), tare da samar da kuɗaɗe masu sassaucin ƙa’idoji ga ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi, da ƙara ƙarfin muradun ci gaba mai ɗorewa (SDGs) a ƙasashen Afirka da dama.

  • Rikicin Gabar Yammacin Kogin Jordan: Falasdinu Ta Kawo Karshen Hulda Da Isra’ila

Dangane da manufofin Majalisar Ɗinkin Duniya, BRI na ci gaba da tallafa wa ɗimbin ƙasashe masu tasowa a yunkurinsu na samun ci gaba mai ɗorewa, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ke kallonsa a matsayin wani muhimmin jagoranci kan ci gaban fasaha.

Tuni MDD ta yi gargadin cewa, alfanun irin wannan sauyi ya karkata sosai zuwa ga ƙasashe masu arziki, yana mai jaddada muhimmancin kiyaye ƙarin “abokan haɗin gwiwa” da ƙasar Sin, don taimakawa wajen cimma burin SDG.

A matsayinta na ƙasa mai tasowa mafi girma, Sin ta fahimci muhimmancin jagoranci kan kare hakkin dan Adam da daidaiton jinsi. A gun taron kwamitin kare hakkin bil adama na MDD karo na 53 da aka gudanar, ƙasar Sin ta yi na’am da kiraye-kirayen da ƙasashe kusan 80 suka yi na ƙarfafa haɗin kai, maimakon rarrabuwar kawuna, wajen tinkarar ƙalubalen hakkin dan Adam.

Labarai Masu Nasaba

Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai

Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus

Hakazalika, ra’ayin Sin game da ’yancin ɗan adam ya samar da gagarumar nasara a kan yaƙi da matsananciyar talauci, musamman ga ƙasar da ta kai kusan kashi biyar na al’ummar duniya, bisa la’akari da irin wannan fa’ida, ƙasar Sin ta bude wani sabon salo na haɗin gwiwar raya ƙasa tare da MDD, wanda ya ƙunshi shigar da ’yan kasuwa sama da 650 na ƙasar Sin a cikin yarjejeniyar duniya ta MDD kan ’yancin dan Adam, da samar da ayyukan yi, da muhalli da yaƙi da cin hanci da rashawa.

Yayin da ake fuskantar barazanar koma bayan tattalin arziki, da rashin tabbas na ci gaba, da rikice-rikice masu yawa, yana da matuƙar muhimmanci ga MDD da Sin su zurfafa alaƙa, da magance giɓin da ake samu wajen zaman lafiya, da ci gaba da shugabanci.

Shirin raya ƙasa da ƙasa (GDI) da ƙasar Sin ke jagoranta, shi ma wani kyakkyawan misali ne na ci gaban da aka samu tare. Majalisar Ɗinkin Duniya ta tallafa wa asusun haɗin gwiwar kudu-maso-kudu na GDI, albarkatun da ke baiwa ƙasashe damar shawo kan matsalolin kuɗi da kuma kawo cikas ga maƙasudan ci gaba mai ɗorewa.

A yayin da ɓangarorin biyu ke ƙoƙarin yin haɗin gwiwa kan ayyukan sauyin yanayi a duniya, goyon bayan da ƙasar Sin ta bayar na haɗin gwiwa a fannin makamashi mai tsafta a duniya, wata shaida ce ta yaƙi da rikice-rikicen da ake fuskanta.

Ƙarfafa haɗin gwiwa tare da Sin a fannoni daban-daban, ya sake jadadda wannan batu na cewa, “Haɗin gwiwar Sin da Majalisar Ɗinkin Duniya na da tasiri ga makomar zaman lafiyar duniya”. (Yahaya Babs)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Sin Za Ta Kara Samar Da Dama Ga Duniya A Fannin Kasuwanci

Next Post

Gwamnan Kebbi Ya Kori Hadiminsa Kan Wallafa Wani Sako A Kafafen Sada Zumunta

Related

Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai
Daga Birnin Sin

Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai

2 hours ago
Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus

3 hours ago
Sin: Batun Taiwan Sha’ani Ne Na Cikin Gidan Kasar Sin Kuma Bai Yi Kama Da Rikicin Ukraine Ba
Daga Birnin Sin

Sin: Batun Taiwan Sha’ani Ne Na Cikin Gidan Kasar Sin Kuma Bai Yi Kama Da Rikicin Ukraine Ba

4 hours ago
Darajar Hajojin Da Aka Fitar Waje Daga Birnin Shanghai Ta Kai Yuan Biliyan 629 Cikin Watanni Hudu Na Farkon Shekarar Bana
Daga Birnin Sin

Darajar Hajojin Da Aka Fitar Waje Daga Birnin Shanghai Ta Kai Yuan Biliyan 629 Cikin Watanni Hudu Na Farkon Shekarar Bana

6 hours ago
Babban Sauyi Da Ba a Taba Ganin Irinsa Ba a Karni Guda: Alkiblar Da Sin Take Bi Wajen Samun Bunkasuwa 
Daga Birnin Sin

Babban Sauyi Da Ba a Taba Ganin Irinsa Ba a Karni Guda: Alkiblar Da Sin Take Bi Wajen Samun Bunkasuwa 

8 hours ago
Wang Yi Ya Gana Da Sabon Jakadan Amurka A Sin
Daga Birnin Sin

Wang Yi Ya Gana Da Sabon Jakadan Amurka A Sin

9 hours ago
Next Post
Gwamnan Kebbi Ya Kori Hadiminsa Kan Wallafa Wani Sako A Kafafen Sada Zumunta

Gwamnan Kebbi Ya Kori Hadiminsa Kan Wallafa Wani Sako A Kafafen Sada Zumunta

LABARAI MASU NASABA

Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai

Zaman Lafiya A Duniya: Mu Baje Sin Da Amurka A Faifai

June 4, 2025
Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus

Shugaba Xi Ya Gana Da Takwaransa Na Belarus

June 4, 2025
Sin: Batun Taiwan Sha’ani Ne Na Cikin Gidan Kasar Sin Kuma Bai Yi Kama Da Rikicin Ukraine Ba

Sin: Batun Taiwan Sha’ani Ne Na Cikin Gidan Kasar Sin Kuma Bai Yi Kama Da Rikicin Ukraine Ba

June 4, 2025
Kotu Ta Tura Ɗan Tiktok Gidan Yari Kan Shigar Mata Da Kalaman Batsa A Kano

Kotu Ta Tura Ɗan Tiktok Gidan Yari Kan Shigar Mata Da Kalaman Batsa A Kano

June 4, 2025
‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri 4, Sun Ƙwato Makamai A Filato

June 4, 2025
Darajar Hajojin Da Aka Fitar Waje Daga Birnin Shanghai Ta Kai Yuan Biliyan 629 Cikin Watanni Hudu Na Farkon Shekarar Bana

Darajar Hajojin Da Aka Fitar Waje Daga Birnin Shanghai Ta Kai Yuan Biliyan 629 Cikin Watanni Hudu Na Farkon Shekarar Bana

June 4, 2025
Babban Sauyi Da Ba a Taba Ganin Irinsa Ba a Karni Guda: Alkiblar Da Sin Take Bi Wajen Samun Bunkasuwa 

Babban Sauyi Da Ba a Taba Ganin Irinsa Ba a Karni Guda: Alkiblar Da Sin Take Bi Wajen Samun Bunkasuwa 

June 4, 2025
‘Yansanda Sun Kama Mutane 2 Da Makamai Masu Yawa A Jihar Nasarawa

‘Yansanda Sun Kama Mutane 2 Da Makamai Masu Yawa A Jihar Nasarawa

June 4, 2025
Wang Yi Ya Gana Da Sabon Jakadan Amurka A Sin

Wang Yi Ya Gana Da Sabon Jakadan Amurka A Sin

June 4, 2025
Garkuwa: Sarkin Gobir Ya Bukaci Agajin Gaggawa Daga Gwamnatin Sakkwato

Mutum 7 Sun Rasu Sakamakon Kifewar Kwale-kwale A Sakkwato 

June 4, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.