Wata kotun tarayya da ke birnin tarayya, Abuja ta dakatar da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), daga gurfanar da kwamshinan zaben Jihar Adamawa da aka dakatar, Hudu Yunusa Ari kan ayyana Aisha Dahiru Binani, ta jam’iyyar APC a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.
Mai shari’a Donatus Okorowo, ne ya bayar da umarnin bayan da lauyan da ke kare Binani Mista Michael Aondoaka, SAN, ya gabatar da bukatar hakan.
- Kano: Kotu Ta Kori Karar Da Ke Kalubalantar Nasarar Alhassan Rurum
- Abba Ya Sake Nada Sheikh Daurawa Shugaban Hisbah Ta Kano
A cikin bukatar da suka gabatar, ‘yar takarar gwamnan APC, ta shigar da INEC da babban mai shari’a na kasa kara.
Yayin da ya ke gabatar da bukatar a ranar Litinin, Aondoaka ya ce kamata ya yi har sai kotu ta tabbatar da matsayin wadda ya ke karewa kamar yadda sashe na 149 na kundin zaben 2022 ya tanadar, kafin a gurfanar da Yunusa Ari.
Ya ce sun rubutawa kotu don nuna mata cewa karar da suka kai mai karfi ce.
Ya ce a cikin takardar da suka rubuta sun ce sun amince cewa za su amince da duk wani hukunci kotu idan aka tabbatar da cewa karar ba mai karfi ba ce.
Idan ba a manta ba Ari ya ayyana Binani a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan Adamawa tun kafin a kammala tattare sakamakon zaben.
Lamarin da ya jefa dubban mutanen kasar nan cikin rudani da tafka muhawara mai zafi.