Kwanakin baya, wasu dalibai ’yan Najeriya 65 sun kammala karatu a kasar Sin, sun kuma koma gida. Bisa tallafin da wani kamfanin kasar Sin ya ba su, wadannan dalibai sun gama karatun ilimin injiniyan gini, da fannin jigilar kayayyaki a jami’o’in kasar Sin, inda suka samu digiri na farko ko na biyu. Galibinsu za su fara aiki a kamfanonin kasar Sin dake Najeriya, inda za su samar da gudunmowa ga aikin raya masana’antu masu alaka da zirga-zirgar jiragen kasa a kasarsu ta Najeriya.
Batun nan ya nuna sahihancin kasar Sin a fannin taimakawa Najeriya wajen samun ci gaba. Ban da daukar nauyin gina layin dogo na Abuja-Kano, da na Lagos-Ibadan, da layin jirgin kasa a birnin Abuja, da dai sauran ingantattun kayayyakin more rayuwa a Najeriya, kasar Sin ta kuma ba da taimako a fannin horar da kwararrun da suka san yadda ake sarrafawa da kulawa da kayayyakin. Ban da haka kuma, kasar ta mika wa matasan Najeriya damammaki na samun ilimi, da guraben aikin yi, da na cimma manyan burikan da suka sanya a gaba.
Hakika, idan mun yi tsokaci kan manufofin kasar Sin na hulda da sauran kasashe, za mu ga yadda “more ci gaba tare” ya kasance wani muhimmin bangare a cikinsu. Cikin “shawarar neman samun ci gaba a duk duniya” wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, ya ambaci fannonin da suka hada da taimakawa sauran kasashe masu tasowa samun ci gaban tattalin arziki, da kyautata zaman rayuwar jama’arsu, da hadin kai da sauran kasashe a kokarin rage talauci, da tabbatar da samar da isashen abinci, da samar da jarin da ake bukata don neman ci gaba, da raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, da raya masana’antu, da dai makamantansu.
Ban da haka kuma, kasar Sin ta daukaka tunanin “Kyan alkawari cikawa”. Tun da ta ba da shawarar “more ci gaba tare”, to, dole ne ta yi kokarin aiwatar da manufar. Game da haka, za a iya duba abubuwan dake faruwa a dab da mu, wadanda suka kasance misalai ga yadda hadin gwiwa tare da kasar Sin ke haifar da ci gaba ga kasashen Afirka:
A kasar Mauritius dake gabashin Afirka, wani kamfanin kasar Sin ya gina wata madatsar ruwa a dab da birnin Port Louis na kasar, wadda ta kawo karshen matsalar karancin ruwa da birnin ke fuskanta, ta yadda mazauna wurin suke iya samun ruwan famfo. Wannan shi ne misalin yadda ake samun ingantuwar zaman rayuwar jama’a.
A kasar Kenya kuma, layin dogon da aka gina a tsakanin Mombasa da Nairobi, ya rage lokacin zirga-zirga a tsakanin biranen daga sa’o’i 10 zuwa sa’o’i 4. Ya kuma sanya ‘yan kasuwan kasar murna sosai, domin kudin da suke kashewa wajen jigilar kaya ya ragu da kashi 79%. Hakan misali ne na kyautatuwar muhallin ciniki, da aka samu ta hanyar hadin gwiwa da kasar Sin.
Haka zalika, cikin shekaru fiye da goma da suka gabata, ta hanyar gudanar da kwas na gajeren lokaci, kasar Sin ta taimaki kasashen Afirka wajen horar da mutane fiye da dubu 300, wadanda suka zama kwararru a fannonin aikin gona, da kula da itatuwa, da kare muhalli, da dai sauransu. Wannan ya nuna yadda kasar Sin take taimakawa kasashen Afirka wajen samun karfin raya tattalin arziki ta hanyar dogaro da kai.
Ko a nahiyar Afirka, ko a sauran wurare da kusurwoyin duniya, za a iya ganin dimbin misalai iri daya da wadanda muka ambata. Sai dai me ya sa kasar Sin ke son yayata ra’ayin “more ci gaba tare” a duniya?
Dalilin da ya sa haka shi ne al’adun gargajiyar kasar. Kaka da kakanin Sinawa, musamman ma wasu shahararrun malamai masu ilimi sun taba bayyana cewa, “ Duk wani abun da ba ka so, kar ka yi shi kan sauran mutane”, kana “ Mutum mai kirki ya fi dora muhimmanci kan kare adalci maimakon moriyar kai”. Ban da haka kuma, sun ce, “A yayin da kake kula da tsoffi da yara dake gidanka, kar ka manta da taimakon tsoffi da yara na gidajen sauran mutane.” Wannan tunani da al’adu mai alaka da shi sun sa Sinawa darajanta yanayin daidato, da adalci, da more alheri tare, gami da samun jituwa.
Sa’an nan wannan nau’in al’adu na gargajiya ya tabbatar da cewa, kasar Sin ba za ta mai da moriyar kanta a gaban ta sauran kasashe ba, kuma ba za ta taba neman yin babakere a duniya ba. Bayan da kasar ta samu nasarar raya kanta daga wata kasa mai talauci zuwa kasa mai karfin tattalin arziki tattalin arziki ta biyu a duniya, tare da samun dimbin fasahohi a fannin neman ci gaba, kasar na kuma son raba fasahohinta da sauran kasashe, da hadin gwiwa da su don neman damar samun ci gaban tattalin arziki na bai daya. Saboda bisa tunanin Sinawa, duniya ba za ta zama mai kyau ba, har sai an tabbatar da dadaito, da zaman lafiya, da more ci gaba, da wayewar kai a cikinta. (Bello Wang)