Babban sakatare a kungiyar kwadago ta manoman kasar Ghana Edward mareweh, ya ce Ghana da sauran kasashe masu tasowa, za su iya koyi daga muhimmin darashin da kasar Sin ta samar, daga ci gaban ta a fannin bunkasa noma da rage talauci.
Yayin wata tattaunawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan nan, Kareweh ya ce kwazon kasar Sin a wadannan fannoni na zaburar da sauran kasashe masu tasowa. Ya ce, “Sin na cimma manyan nasarori a fannin tsame al’ummun ta daga fatara. Duk da cewa kaso mai tsoka na al’ummar Sinawa manoma ne, kwatankwacin yanayin da muke da shi a nan, amma sakamakon aiki tukuru, gwamnatin kasar Sin ta yi nasarar fitar da al’ummun ta daga matsanancin talauci”.
Daga nan sai jami’in ya alakanta nasarar da Sin din ta samu, da yadda gwamnatin kasar ke sanya ci gaban al’umma, da moriyar su gaban komai, wanda hakan ke haskakawa Ghana, da ma sauran kasashen Afirka dabarun inganta noma da shawo kan kalubalen talauci. (Mai fassara: Saminu Alhassan)