Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar dattawa ta amince da bukatar karbo bashin dala miliyan 800 don amfani da su wajen rage wa talakawa radadin cire tallafin man fetur.
Bukatar shugaban ta kasance a cikin wata wasika da Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa ya karanta a zauren majalisar a ranar Alhamis.
- Kotu Ta Umarci DSS Ta Saki Emefiele Cikin Mako Daya
- Na Yafe Wa Kowa, Ina Rokon Yafiyar Kowa —Sheikh Dahiru Bauchi
Tinubu ya bayyana cewa za a yi amfani da rancen ne wajen habaka shirin samar da zaman lafiya a kasar nan.
Ya ce sabon rancen za a karbo shi ne daga Bankin Duniya.
Ya kuma ba da tabbacin gwamnatin tarayya za ta biya Naira 8,000 duk wata ga marasa karfi mutum miliyan 12 na tsawon watanni shida.
Ya ce za a tura kudaden ne kai tsaye zuwa asusun wadanda za su amfana da su.
Tun da fari shugaba Tinubu ya bukaci majalisa ta amince masa ya karbo rance don rage radadin cire tallafin man fetur fa ya yi.
Idan za a tuna a ranar 29 ga watan Mayu 2023, Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur a jawabinsa na karbar mulki.
Lamarin da ya sanya farashin man fetur yin tashin gwauron zabi.