Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya amince da fara amfani da asusun bai-daya don tabbatar da gaskiya da adalci a ayyukan gwamnati.
A kan wannan, gwamnatin jiha ta dakatar da dukkan hada-hadar kudade ta asusun ajiya na kudaden shiga daga ma’aikatu da sassa da hukumomi daban-daban.
- Wane Ne Arda Guler Mai Lakabin ‘Sabon Messi A Real Madrid’?
- Sin Na Cika Alkawuranta Na Hadin Gwiwar Raya Kiwon Lafiya Ga Kasashen Afirka
Mataimakin gwamna Malam Faruk Lawal Jobe ya bayyana haka a lokacin taron manema labarai da ya gudana a cibiyar ‘yan jarida ta ofishin mataimakin gwamna.
Malam Faruk Lawal Jobe ya bayyana cewa an shirya taron manema labarai ne domin yin karin haske a kan manufofi da tsare-tsaren gwamnati. Ya ce ya zama wajibi dukkanin kudaden shigar da jihar ta samu a zuba su zuwa asusun bai-daya, yayin da ma’aikatu da sassa da hukumomi ya zama tilas su nemi izini kafin cire kudaden.
Haka kuma ya bayyana cewa za a kafa kwalejin ma’aikata domin horas da ma’aikatan gwamnati. Ya ce ya zama wajibi ga ma’aikaci daga mataki na 13 ya rubuta jarrabawa kafin a yi masa karin girma zuwa mataki na gaba.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa sakamakon jarrabawar da manyan sakatarori suka gudanar ya fito, inda ake dakon rahoton kwamitin da ya gudanar da aikin.
Hakazalika, gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda ya karbi bakuncin kamfanonin karbar haraji guda 7 domin tattauna yadda za su bayar da gudummuwa ga hukumar tattara kudaden shiga ta jihar.
Gwamnan ya bayyana godiyarsa ga kwararru bisa amfani da ilimi da kuma kwarewar da suke da ita wajen tallafa wa hukumar tattara kudaden shiga ta Jihar Katsina wajen zamanantar da ayyukanta a bangarori daban-daban.