Wani rahoto da kafar yada labarai ta BBC Hausa ta fitar ya bayyana yadda mutane suke ta daga kai sama cikin al’ajabi lokacin da wata ya bayyana cikin haske da girma fiye da yadda aka saba gani da daddare.
A cewar hukumar binciken sararin samaniyan Amurka ta NASA, ana ganin hamshakin watan da ke bayyana a cikin Yuli, da siffar cikarsa har tsawon sama da kwana uku.
- Gwamna Dikko Ya Amince Da Bude Asusun Bai-daya A Jihar Katsina
- Ribadu Zai Shugabanci Taron LEADERSHIP Da NDLEA Kan Yaki Da Miyagun Kwayoyi
 Watan kan yiwo kasa-kasa fiye da yadda aka saba gani a kan hanyar da yake zagaye Duniyar Az.
Hakan na faruwa ne saboda hanyar da watan yake bi, ba kammalallen zagaye bane sakamakon maganadisun janyo abu kasa da Duniyar Az ke yi, maimakon haka sai ya yi ta katantanwa kamar wani zobe.
 Saboda haka, akwai lokutan da a zagayen kwana 27 da ‘yan sa’o’i da watan ke yi, yana zuwa kusa da Duniyar Az, akwai kuma lokutan da ya kan yi can kololuwar sama.
Ana samun irin wannan hamshakin wata ne, idan watan ya yi wo kusa-kusa sosai da duniyarmu a kan hanyar da yake zagaye.
 A cewar Cibiyar Binciken Sararin Samaniya ta Royal Obserbatory, Amurkawan Asali ne suka yi wa cikakken watan na Yuli, lakabi da sunan ‘Buck Moon’ saboda kahonnin dabbar gwanki na kai wa matukar girmansu a watan Yuli.
Kahonnin suna kadewa sannan wasu suke tsirowa a lokacin.
 Watan ya kai kololuwar haskensa da karfe 12:39 agogon Nijeriya ranar Litinin, a cewar Cibiyar Nazarin Hasashen Yanayi ta Old Farmer’s Almanac.
Cibiyar Almanac din wadda ke wallafa bayanai kan al’amuran ilmin taurari ta ce Hamshakin Watan ya fi kusantar Duniyar Az a zagayen da yake yi idan an kwatanta da cikakkun watannin da muka riga muka gani a wannan shekara.
Cikakken watan Agusta zai kasance hamshakin watan da kawai zai fi kusa da Duniyar Az a wannan shekara, in ji cibiyar.
Ga dai wasu wurare da Hamshakin wata ya gibta
Hamshakin watan ya haskaka shudiyar samaniya lokacin da ya daga ta saman hasumiyar fitilu a tsibirin St Mary cikin garin Whitley Bay na lardin Tyne and Wear da ke Arewa maso Gabashin Ingila ranar Lahadi.
Watan ya yi launin ruwan goro inda ya haska sama cikin duhun dare a yankin Stockingford cikin lardin Warwickshire na Ingila.
Wata tarakta tana aiki a gona cikin tsakiyar hasken watan a kusa da birnin Ashkelon da ke kudancin Isra’ila ranar Litinin.
Hamshakin watan ya yiwo kasa-kasa a kauyen Seaton Sluice na lardin Northumberland a Burtaniya.
 Cikakken watan yana faduwa ta bayan Shudin Masallaci (Blue Moskue) da kuma Kasaitaccen Masallacin Hagia Sophia na birnin Santambul a Kasar Turkiyya.
Mashahurin Mutum-mutumin Statue of Liberty na birnin New York a Amurka shi ma ya jera da hamshakin watan a sama.
Wani jirgin sama da aka dau hotonsa yana wucewa ta jikin hamshakin watan a saman birnin Paris, ‘Yan kallon da suka taru don ganin wata gasar wasanni ga dukkan alamu ba su ma lura da cikakken watan da ke bayansu ba a birnin Kutaisi na Kasar Georgia.
 Watan ya yiwo kasa-kasa har daidai kan Majami’ar Birgin Mary Chaldean da ke birnin Basra na Kasar Iraki.
An yi arba da hamshakin watan a kusa da wata fitilar kan titi a birnin L’Akuila na Kasar Italiya
Wani tsuntsu na giftawa ta kusa da hamshakin watan lokacin da ya dago sama daidai kan hasumiyar fitilu a tashar jirgin ruwa ta Malaga cikin Kasar Sifaniya.