ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 16, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Wani Hamshakin Wata Ya Bayyana A Sararin Samaniyar Duniya

by Rabi'u Ali Indabawa
3 years ago
Duniya

Wani rahoto da kafar yada labarai ta BBC Hausa ta fitar ya bayyana yadda mutane suke ta daga kai sama cikin al’ajabi lokacin da wata ya bayyana cikin haske da girma fiye da yadda aka saba gani da daddare.

A cewar hukumar binciken sararin samaniyan Amurka ta NASA, ana ganin hamshakin watan da ke bayyana a cikin Yuli, da siffar cikarsa har tsawon sama da kwana uku.

  • Gwamna Dikko Ya Amince Da Bude Asusun Bai-daya A Jihar Katsina
  • Ribadu Zai Shugabanci Taron LEADERSHIP Da NDLEA Kan Yaki Da Miyagun Kwayoyi

 Watan kan yiwo kasa-kasa fiye da yadda aka saba gani a kan hanyar da yake zagaye Duniyar Az.

ADVERTISEMENT

Hakan na faruwa ne saboda hanyar da watan yake bi, ba kammalallen zagaye bane sakamakon maganadisun janyo abu kasa da Duniyar Az ke yi, maimakon haka sai ya yi ta katantanwa kamar wani zobe.

 Saboda haka, akwai lokutan da a zagayen kwana 27 da ‘yan sa’o’i da watan ke yi, yana zuwa kusa da Duniyar Az, akwai kuma lokutan da ya kan yi can kololuwar sama.

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

Ana samun irin wannan hamshakin wata ne, idan watan ya yi wo kusa-kusa sosai da duniyarmu a kan hanyar da yake zagaye.

 A cewar Cibiyar Binciken Sararin Samaniya ta Royal Obserbatory, Amurkawan Asali ne suka yi wa cikakken watan na Yuli, lakabi da sunan ‘Buck Moon’ saboda kahonnin dabbar gwanki na kai wa matukar girmansu a watan Yuli.

Kahonnin suna kadewa sannan wasu suke tsirowa a lokacin.

 Watan ya kai kololuwar haskensa da karfe 12:39 agogon Nijeriya ranar Litinin, a cewar Cibiyar Nazarin Hasashen Yanayi ta Old Farmer’s Almanac.

Cibiyar Almanac din wadda ke wallafa bayanai kan al’amuran ilmin taurari ta ce Hamshakin Watan ya fi kusantar Duniyar Az a zagayen da yake yi idan an kwatanta da cikakkun watannin da muka riga muka gani a wannan shekara.

Cikakken watan Agusta zai kasance hamshakin watan da kawai zai fi kusa da Duniyar Az a wannan shekara, in ji cibiyar.

Ga dai wasu wurare da Hamshakin wata ya gibta

Hamshakin watan ya haskaka shudiyar samaniya lokacin da ya daga ta saman hasumiyar fitilu a tsibirin St Mary cikin garin Whitley Bay na lardin Tyne and Wear da ke Arewa maso Gabashin Ingila ranar Lahadi.

Watan ya yi launin ruwan goro inda ya haska sama cikin duhun dare a yankin Stockingford cikin lardin Warwickshire na Ingila.

Wata tarakta tana aiki a gona cikin tsakiyar hasken watan a kusa da birnin Ashkelon da ke kudancin Isra’ila ranar Litinin.

Hamshakin watan ya yiwo kasa-kasa a kauyen Seaton Sluice na lardin Northumberland a Burtaniya.

 Cikakken watan yana faduwa ta bayan Shudin Masallaci (Blue Moskue) da kuma Kasaitaccen Masallacin Hagia Sophia na birnin Santambul a Kasar Turkiyya.

Mashahurin Mutum-mutumin Statue of Liberty na birnin New York a Amurka shi ma ya jera da hamshakin watan a sama.

Wani jirgin sama da aka dau hotonsa yana wucewa ta jikin hamshakin watan a saman birnin Paris, ‘Yan kallon da suka taru don ganin wata gasar wasanni ga dukkan alamu ba su ma lura da cikakken watan da ke bayansu ba a birnin Kutaisi na Kasar Georgia.

 Watan ya yiwo kasa-kasa har daidai kan Majami’ar Birgin Mary Chaldean da ke birnin Basra na Kasar Iraki.

An yi arba da hamshakin watan a kusa da wata fitilar kan titi a birnin L’Akuila na Kasar Italiya

Wani tsuntsu na giftawa ta kusa da hamshakin watan lokacin da ya dago sama daidai kan hasumiyar fitilu a tashar jirgin ruwa ta Malaga cikin Kasar Sifaniya.

Duniya
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Wasu Fusatattun Mutane Sun Lakaɗa Wa Mutum Biyu Duka Har Lahira A Kaduna
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan

MASU ALAKA

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya
Labarai

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Sabbin Ministoci
Labarai

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 
Labarai

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Next Post
Masani Habasha Ya Yi Karin Haske Kan Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

Masani Habasha Ya Yi Karin Haske Kan Zurfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Sin Da Afirka

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

Binciken CGTN: Amfanar Da Kowa Da Kowa Shi Ne Ainihin Alherin Da Fasahohin Kwaikwayon Tunanin Bil Adama Suka Kawo

July 15, 2026
Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Sin Ta Yi Kira Da A Kafa Tsarin Jagorantar Muhimman Ma’adinai Ga Sauyawa Zuwa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

July 15, 2026
Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

Gwamna Dauda Lawal Zai Gabatar Da Jawabi A Taron Ƙasa Da Ƙasa Na Jami’ar FUE Zariya

July 15, 2026
Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

Neman Raba-Gari Da Sauran Kasashe Zai Kawo Mummuann Tasiri Ga Bangarorin Da Abin Ya Shafa

July 15, 2026
Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

Kevin Kelly: AI Na Iya Taimakawa Wajen Cimma Burin “Koyar Da Dalibai Da Kwazonsu”

July 15, 2026
Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

Gwamna Yusuf Ya Bai Wa Masu Kula Da Akwatinan Zaɓe Na APC Filaye 1,540 Da Tallafin Miliyan 100

July 15, 2026
Sabbin Ministoci

Rashin Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Tura Ƙarin Sojoji da ’Yansanda Zuwa Benuwe

July 15, 2026
GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

GDPn Sin A Rabin Farko Na Shekarar 2026 Ya Karu Da Kashi 4.7% Idan Aka Kwatanta Da Na Kwatankwacin Lokacin Bara

July 15, 2026
‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga 

Atiku Ya Nuna Damuwa Kan Kasafin Naira Biliyan 6.44 Don Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026

July 15, 2026
Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

Masana Kandagarkin Cututtuka Na Sin Sun Tashi Zuwa Kasar Uganda Don Aikin Hadin Gwiwar Magance Cutar Ebola

July 15, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.