Taken fim din da aka yi bisa dogaro da labarin karen shi ne: ” Zan jira ka komai tsawon lokaci.”
Labari ne na Hachiko, wani kare da ya kwashe shekaru yana jiran dawowar maigidansa.
Karen mai launin fari, wanda aka haifa shekaru 100 da suka gabata, an yi fina-finai da rubuce-rubuce don bayar da labarinsa wanda ya kunshi al`adun al`ummar Chaina, a shekara ta 1987, an yi wani fim sannan a shekara ta 2009 jarumi Richard Gere ya fito a jigon wani fim da ya yi fice mai dauke da labarin Hachiko.
Akwai wasu labarun na karnukan da suka yi abubuwan al`ajabi da sadaukarwa ga iyayen gidansu, kamar karen nan mai suna Greyfriars Bobby to amma babu karen da labarinsa ya shahara a duniya kamar Hachiko.
An girke mutum-mutumin Hachinko na tagulla a kofar tashar Shibuya da ke Tokyo, inda karen ya yi zaman jiran Ubangidansa na tsawon lokaci.
An fara kafa mutum-mutumin a shekara ta 1934 kafin a canja shi bayan yakin duniya na biyu, ana koyar da dalibai a Japan labarin Chuken Hachiko ko Hachiko Karen Alkawari a matsayin misalin amana da sadaukarwa.
Farfesa Christine Yano ta Jami’ar Hawaii ta ce Hachiko yana wakiltar “amintaccen dan Kasar Japan” la`akari da irin rikon amanarsa da cika alkawari da kuma biyayya ga Ubangidansa.
Labarin Hachiko
An haifi Hachiko a watan Nuwamba shekara ta 1923 a birnin Odate da ke Lardin Akita, a asalin gidan Akitas.
Kare ne mai girman jiki dan Kasar Japan, Akita daya ne daga cikin nau`in tsoffin karnukan da suka yi fice. Wadanda Gwamnatin Japan ta zabe su a matsayin alamar kasar a shekara ta 1931, an taba horar da su don farautar dabbobin daji.
“Karnukan Akita suna da natsuwa da amana da hankali da jarumtaka da kuma biyayya ga iyayen gidansu,” in ji Eietsu Sakuraba, marubucin gejerun labarai don yara a harshen Turanci.
Ya kuma bayyana cewar Karnukan su na da dabi`ar taurin kai da kuma taka-tsan-tsan da duk wanda ba Ubangidansu ba.
A shekarar da aka haifi Hachiko, Hidesaburo Ueno, wani mashahurin Farfesa a fannin noma kuma mai son karnuka ya nemi wani dalibi ya samo masa dan kwikwiyon Akita.
Bayan doguwar tafiya a jirgin kasa, dan kwikwiyon ya isa gidan Ueno a gundumar Shibuya ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1924, da farko an yi tsammanin karen ya mutu.
Marubucin tarihin Hachiko Farfesa Mayumi Itoh, ya bayyana cewar Ueno da matarsa, Ya ce sun yi jinyar karen har zuwa lokacin da ya murmure a tsawon watanni shida.
Ueno ya rada masa suna Hachi, ma`ana takwas ke nan a harshen Japan, ko kuma lakabi ne na girmamawa da daliban Ueno suka rada masa.
Dogon Jira
Ueno ya na shiga jirgin kasa sau da dama a mako kuma yana tafiya ne da karnuka 3 da suka hada da Hachiko, haka karnukan suke zaman jiransa har ya dawo da maraice.
A ranar 21 ga watan Mayu shekara ta 1925 a lokacin Ueno yana da shekaru 53 da haihuwa sai ya mutu sakamako ciwo a lakarsa, a lokacin Hachiko yana da watanni goma sha shida tare da su.
Farfesa Itoh ya bayyana cewar yayin da jama`a suke zaman alhinin mutuwar mamacin, sai Hachi ya jiyo kamshin Ubangidansa Dakta Ueno daga cikin gida don haka sai ya kutsa cikin gidan ya shiga karkashin makarar da aka sanya Ueno ya ki fitowa.
Hachiko ya rayu da iyalai daban-daban bayan mutuwar Ubangidansa a wajen gundumar Shibuya amma daga karshe a shekara ta 1928 ya koma gurin Kikusaburo Kobayashi mai kula da furannin ubangidansa.
Ganin ya koma inda Ubangidansa ya rayu, sai Hachiko ya koma sintiri zuwa tashar jiragen kasa kullum komai ruwa komai zafin rana.
Ya shahara a kasar bayan Jaridar Asahi Shimbun ta fitar da wani labarinsa a watan Oktoban shekara ta 1932.
Tashar Jiragen kasan ta samu gudummawar abincin Hachiko na kowacce rana, yayin da baki suke zuwa don ganinsa, an rubuta kasidu da dama game da shi.
A shekara ta 1934 an kaddamar da gidauniyar kera mutum-mutuminsa, wacce ta samu halartar mutane akalla dubu uku.
Hachiko ya mutu a ranar 8 ga watan Maris shekara ta 1935, labarin da Jaridu da dama suka buga, shugabannin Addinin Buddha sun yi masa da addu`o`i yayin da dubban mutane suka ziyarci mutum-mutuminsa.
Tunawa da Hachiko
Kowace shekara a ranar 8 ga watan Afrilu, ana gudanar da taron tunawa da Hachiko a tashar Shibuya, a lokaci ana yi wa mutum-mutuminsa ado da gyale da hular Santa da kuma kuma takunkumin rufe fuska.
Shin ko za a ci gaba da bikin tunawa da kare mafi rikon alkawari a duniya shekaru dari daga yanzu? Farfesa Yano ta ce labarin “jarumtar Hachiko” ba ya da lokacin karewa.
Shi ma Mista Sakuraba yana da kyakkyawan fatan labarin Hachiko zai dore har abada. Mun ciro daga BBC HAUSA