Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga masana, da kwararru dake a fannonin kimiyya da fasaha, da su janyo karin ma’aikata a fannonin su, ta yadda za a kara yayata ilimin kimiyya, da kyautata wayewar kai tsakanin al’umma game da fannin.
Kaza lika, ya bukace su da su ci gaba da ba da gudummawa, wajen cimma burin da ake da shi na kaiwa ga dogaro da kai a manyan fannonin kimiyya da fasaha, da ingiza nasarar salon zamanantarwa irin ta Sin.
Xi Jinping ya yi wannan kira ne a jiya Alhamis, cikin wata wasika da ya aike a matsayin amsa, ga wasikar gungun masana da kwararru a fannonin kimiyya da fasaha, wadanda ke halartar wani taron karawa juna sani mai taken “Kimiyya da Sin.” (Saminu Alhassan)