Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta ware ranar 3 ga watan Agusta a matsayin ranar da za ta kammala jigilar dawo da alhazan Nijeriya daga kasa mai tsarki.
Wannan tabbacin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta samu dawo da alhazan 45,000 daga cikin alhazai 75,000 da suka je Saudi Arabiyya don sauke faralin hajji da suka tafi ta hannun hukumar da hukumomin kula da alhazai na Jihohi cikin jirage 114.
- ‘Yansanda Sun Cafke Daliban Jami’a 3 Kan Kashe Direban Mota
- Halin ‘Yan Siyasa Na Ba Sarakuna Mamaki – Sarkin Zazzau
A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai na hukumar, Alhaji Mousa Ubandanwaki, ya fitar, ya ce, aikin jigilar alhazan karo na biyu da aka fara a ranar 4 ga watan Yulin 2023 da ya kwaso alhazan jihar Sokoto 387 fa kamfanin Flynas ya yi, daga baya kuma kamfanonin jirgi na – Max Air, Flynas, Aero da Azman za su kammala kwaso sauran.
Sanarwar ta ce an samu matsalolin da suka bijiro sakamakon wasu kujerun da suka karu ba tare da suna cikin tsari ba, amma daga bisani shugaban hukumar NAHCON Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da hukumomin Nijeriya sun tabbatar da shawo kan matsalolin kuma aikin jigilar yanzu na cigaba da tafiya yadda ya dace.
Shugaban NAHCON ya yaba wa hukumomin kasar Saudiyya da kamfanonin jiragen sama bisa kokarinsu na ganin an samu nasarar kammala jigilar cikin kwanciyar hankali. Ya bukaci kowani bangare da su cigaba da bada hadin kai.