Inji Matawalle, gwamnan Jihar Zamfara. Ya ce, jama’a fa su dau bindiga su kare kansu daga barnar ‘yan bindiga a fadin Jihar.
Ya kamata a kira taron gaggawa na majalisar dinkin duniya, a sanar musu cewa a Nijeriya, kasar da ake karyar giwar Afirka, a Jihar Zamfara inda ‘yan fasa-kauri daga kasashen duniya suke satar ma’adinai – gwamna ya bada umurnin talakawansa su dau bindiga.
A gabadaya kananan hukumomi 14 na Zamfara babu karamar hukuma guda daya da babu barnar ‘yan binidga, hatta a babban birnin jihar, wato Gusau, kana yin kasake kaman gaula, za a sace ka, babu ruwansu su ‘yan bindigan.
Kafin a fara sata da fasa kaurin ma’adinai a Jihar Zamfara, babban abin da al’ummar Jihar suna tinkaho da takama ne da noma, ma’ana da shi suke yin arziki har su iya hada kafada da sauran attijiran Nijeriya, su yi aure, su gina gidajen alfarma, su je Hajji, su yi layya, su yi tuwo da miyar sallah. Bayan attijarai da suke kasuwanci da noma, sauran al’umma wato talakawa da noma suka dogara don shuka abin da za su ci na tsawon shekara. Wanda ya yi saura kuma su sayar don samun ‘yan canjin biyan kananan bukatu.
Mu koma kan umurnin Gwamna Matawalle na cewa kowa ya dau bindiga. Duk da a bayyane yake ga kowa, amma yana da kyau karin bayani. Ta ya mutanen da suke gudun hijira za su iya daukar bindiga? Ta ina mutanen da aka hana zuwa gonakinsu za su iya daukar bindiga?
Da farko dai wannan bindigar ba a bishiya ake tsinkota ba. Sayar da ita ake a kasuwa, da tsada ma. Mutumin da zai iya mallakar bindiga ta halastacciyar hanya, dole ya zama ya fi karfin abin da zai ci. Da yawan mutanen sun galabaita, ta kansu suke. Da yawa an yi musu koren kare daga kauyukansu, babu muhalli ballantana gonar shuka.
Gwamna Matawalle duk bai yi la’akari da irin wadannan abubuwa ba, na halin kuncin da mafi yawa ke ciki. Wanda zai hana musu ikon mallakar bindigar da ya bada umurnin su dauka don samarwa kansu da kariya. Tunda gwamnatin tarayya da ta Jiha ta gaza.
Akwai abubuwa masu ban tsoro sosai ga wannan sanarwar, kuma dukkan abubuwan sun shafi al’umma ne kaitsaye, sun shafi zamantakewa, tsaro da zaman lafiya.
Na farko, yana nufin kaitsaye babu wani tantama cewa gwamnati ta gaza, kuma babu wani abu da za ta iya yi wurin samar da tsaron rayuka da dukiyar al’ummar Jihar Zamfara, wanda shi ne ginshikiin zamanta hukuma mai cikakken iko. Halastaccen iko shi ne yake bambanta hukuma irin ta Zamfara da hukuma irin ta su dan iskan gari, Turji. Wannan halascin kuwa ya gangaro ne tun daga zabe (halastaccen zabe ne ko magudi) zuwa rantsar da gwamna. Yana nufin akwai wani tsari da aka biyo ta cikinshi wurin samar da gwamnatin. Duk wannan tsarin, ana kiyaye shi ne saboda ita gwamnatin ta kare rayuka da dukiya.
Na biyu, idan makamai suka fara yawo barkatai a cikin jihar Zamfara, za a sha mamaki. Saboda halin kuncin da mutane suka tsinci kansu, ga matsiyacin talauci, babu noma babu aiki. Ita kuma yunwa ba a iya yi mata kawaici, ko da kuwa ana son yi. Mutumin da ke jin yunwa cikin matsanancin kuncin rayuwa, yana iya aikata komi don samun mafita. Akwai mamaki a ce gabadaya masana harkar tsaro da zamantakewar rayuwa da ke tare da Gwamna Matawalle sun kasa fahimtar wannan. Ko don, ba mu sani ba, watakil sun nuna mishi rashin gamsuwa, amma ya cije, tunda gwamna ne.
Yadda ake harkallar satar ma’adanai a Zamfara, idan ya zama kowa na da lasisin daukar bindiga, abin ba zai yi kyau ba. Saboda za a koma rige-rigen kama filayen hako ma’adinai ne, wanda zai sa a rika farmakar juna a tsakanin iyayen daba. Wannan kuma ba yana nufin za a samu zaman lafiya ba ne a Jihar Zamfara, saboda gabadaya rikicin akan dukiya ne ake yin shi. Daga satar Shanu zuwa satar mutane, zuwa satar duk abin da zai yiwu a sata.
Mutane na iya samarwa kansu mafita wurin kare yankunansu ta hanyar yin kwamitin tsaro a matakin unguwanni da sauransu. Wannan zai taimaka musu idan za su ma mallaki bindigar ne, za su yi haka cikin tsarin da duk ranar da wani bako ya zo da mugun nufi za su iya fahimtarshi da manufarsa.
Su kuma wadanda aka tarwatsa daga yankunansu suke gudun hijira a wurare mabambanta, Allah Ya samar musu da mafita ta inda ba su tsammani. Tashin hankalin ya wuce misali, tunda har gwamnati ta gaza, ta ce kowa ya kare kansa. Ko ta ina me harbi ka ruga zai iya fuskantar mai dauke da bindigar da ke sarrafa kanta?