A jiya ne, hukumar ba da agajin gaggawa da hukumar tsaron jama’a na birnin Wuhan na lardin Hubei na kasar Sin, sun ba da sanarwa da rahoton aikin ‘yan sanda bi da bi, inda suka bayyana cewa, cibiyar daidaita kwayar kamfuna cikin gaggawa ta kasar Sin da kamfanin 360 na kasar sun gano cewa, an yi kutse a cibiyar sa ido da bincike girgizar kasa ta birnin Wuhan, masu kutsen ‘yan kungiya ce dake satar bayanai ta kamfuta da masu aikata laifuffuka dake karkashin goyon bayan gwamnati a kasashen waje. Bayan gudanar da cikakken bincike, shaidun farko sun nuna cewa, Amurka ce ta aikata kutsen a wannan karo.
A shekarar 2022, wata kungiyar masu satar bayanai daga ketare, ta kutse a kwamfutocin jami’ar ilmin masana’antu ta Northwest ta Sin wato NPU. A wannan lokaci rahoton bincike ya nuna cewa, ofishin kula da ayyukan kutse ta na’urorin kamfuta wato TAO dake karkashin hukumar tsaron kasar Amurka wato NSA, ya yi amfani da matakan yin kutse ta intanet nau’ikan 41 wajen yin kutse a jami’ar NPU sau fiye da dubu daya, tare da satar wasu muhimman bayanai.
Jami’ar NPU da cibiyar sa ido da bincike girgizar kasa ta birnin Wuhan dukkansu wuraren amfanin jama’a ne, amma Amurka ta sanya musu ido ta hanyar yin kutsen Intanet. A hakika, kasar Amurka tana yunkurin sa ido ga yanar gizo a fadin duniya.
Kasar Sin ta yi Allah wadai da kakkausar murya kan kutsen ta’addanci na Intanet, kuma za ta dauki matakan da suka dace don tabbatar da tsaron yanar gizo. Ya kamata jama’a masu son zaman lafiya a faɗin duniya su ma su hada hannu, tare da nuna adawa da cin zarafi ta yanar gizo da mayar da martani ga kutse ta yanar gizo cikin hadin gwiwa. (Zainab)