Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa tabbas ta samu matsala wurin saka sakamakon zaben shugaban kasa a na’ura, sannan kuma ba ta samu wani taimakon kuda ba daga wurin kowa sai dai gwamnatin tarayya wacce ita ce doka ya daura mata alhakkin yin hakan.
Shughaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu shi ya bayyana hakan a yayin da yake bayar da ba’asi kan na’urar da aka yi amfani da su a lokacin zaben 2023, a lokacin da yake yi wa kungiyoyin fararen huda bayanai kan nazarin zaben 2023.
- ’Yan Bindiga Sun Kashe Shugaban JIBWIS, Sun Sace Mutane 50 A Kaduna
- Badakala A Kano: An Gano Biliyan 4 Da Ta Yi Batan-Dabo A KASCO
Ya kara jaddada cewa abokan hulda sun bayar da tallafi ne kai tsaye ta hanyar kungiyoyin fararen huda wajen gudanar da ayyukan zabe.
Shugaban INEC ya gode wa kungiyoyin farar hula da abokan huda ci bisa gagarumin goyon bayan da suka bai wa hukumar a zaben 2023.
Shugaban na INEC ya tunatar da cewa, kungiyoyi 228 (na gida 190 da 38 na kasashen waje) aka amince da su a matsayin masu sanya ido a zaben da ya gabata, 67 ne kawai suka mika rahotonsu ga hukumar kan zabe.
Ya ce: “A kan wannan lamari, ya dace hukumar ta nuna jin dadinta ga kungiyoyin farar hula da abokan hulda bisa gagarumin goyon bayan da suke bai wa hukumar a lokacin zaben 2023.
Wannan ya zo ne ta hanyar shawarwarin kan fasahar sadarwa da ilimantar da masu jefa kuri’a da gudanar da tarurruka da taron kara wa juna sani da kuma buga takardu.
“A wannan hadin gwiwar ne hukumar ta tantance masu sa ido saboda samun jin ra’ayoyi kan zabe da kuma shawarwarin da suka dace wadanda suke taimaka sosai wajen gudanar da zabe. Domin a zaben shekarar 2023, hukumar ta samu korafe-korafe guda 538 (504 na cikin gida da 34 na kasashen waje) daga wurin masu sa ido. Bayan yin cikakken nazari kan korafe-korafen, kungiyoyi 228 ne kawai (190 na cikin gida da 38 na waje) suka cika ka’idodin da aka zayyana. Sai dai kawo yanzu kungiyoyin sa ido 67 ne (62 na cikin gida da kuma na kasashen waje biyar) suka gabatar da rahoton bincikensu wanda ke wakiltar kusan kashi 30 na kungiyoyin da aka amince da su a zaben. Muna kira ga duk sauran kungiyoyin sa ido da aka amince da su wadanda har yanzu ba su gabatar da rahotonsu ba su yi kokarin gabatar wa hukumar.”
Shugaban INEC ya bayyana cewa an samu nasarar tantance masu kada kuri’a ta hanyar amfani da na’urar BBAS, amma kuma an samu matsala wajen shigar da sakamakon zabe ta intanet ta wannan na’ura.