Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi rangadi a birnin Hanzhong dake lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar a jiya Asabar.
Rangadin na Xi Jinping ya biyo bayan irinsa da ya yi a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, yayin da yake kan hanyarsa ta dawowa Beijing.
Yayin ziyararsa a gidan adana kayayakin tarihi na birnin Hanzhong, Xi ya kara sanin tarihin birnin da al’adunsa, da ma yadda aka kare shi da kayayyakinsa na gargajiya. A cewar shugaba Xi, kayayyakin gargajiya na dauke da wayewar kan jama’a da gadon tarihi da al’adu da daukaka ruhin kasa.
Ya kuma bayyana rawar da gidajen adana kayayyakin tarihi ke takawa wajen kariya da gado da bincike da bayyana wayewar kan bil Adama, da ma fadada kyakkyawan tasirin al’adun kasar Sin a duniya.
Da yake bayyana birnin a matsayin mai dadaddun kuma sanannun al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba da aka yi gado, Xi ya ce ya zama wajibi a raya masana’antu na musammam domin kyautata kudin shiga da ci gaban jama’a.
Yayin rangadinsa a yanki mai damshi dake kusa da kogin Hanjiang na birnin, shugaban ya jaddada muhimmancin kare albarkatu masu damshi na kogin da inganta bayar da cikikkiyar kariya da farfado da muhallan halittun yankuna masu damshi.
Bugu da kari, an labarta cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada bukatar gaggauta kokarin bunkasa zamanantar da rundunar sojin kasar a ranar Larabar da ta gabata a lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin, yayin da yake rangadin aiki a rundunar sojin sama na ’yantar da jama’ar kasar Sin wato PLA ta yammacin kasar.
Shugaba Xi ya yi rangadin ne gabanin ranar murnar cika shekaru 96 da kafuwar rundunar soji ta ’yantar da al’ummar kasar Sin, wato PLA wadda ke gudana a ranar 1 ga watan Augusta. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp