Kungiyar UN International Eminent Peace Ambassador Forum ta karrama Kwanturolan Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS), James Sunday PCC da lambar yabo.
Kungiyar ta karrama shi ne bisa namijin kokari da kwazo da yake yi a hukumar shige da fice ta Nijeriya a matsayin jami’in kasa da kasa lokacin da ya kasance mataimaki na musamman na ministan cikin gida da tsaro.
- Nijar: Sojoji Sun Kame Manyan ‘Yan Siyasa Da Ministocin BazoumÂ
- Barcelona Ta Doke AC Milan A Wasan Sada Zumunta
Wannan na zuwa ne yayin da NIS ke cika shekaru 60 da kafuwa a ranar 1 ga watan Agustan 2023.
Kungiyar ta sanya ido kan yadda yake gudanar da ayyukansa inda ta kuduri aniyar karrama shi don nunawa duniya hidimar da ya jima yana yi.
Kungiyar ta shaida cewar Kwanturolan ya cancanci dukkan yabo, wajen wanzar da zaman lafiya a duk inda ya yi aiki.