Majalisar wakilai ta yi kira ga kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da sauran kungiyoyin da suka yi hadaka da su dakatar da zanga-zangar lumana da suke kan gudanarwa a fadin kasar nan kan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.Â
Majalisar ta yi wannan kiran ne cikin sanarwar da mai magana da yawun majalisar Hon. Akin Rotimi ya fitar.
- Tsohon Shugaban Kasar Ivory Coast, Konan Bedie, Ya Rasu
- Badakalar Biliyan 1.3: EFCC Ta Maka Sule Lamido Da Wasu A Kotun Koli
A cewarsa, maimakon shiga zanga-zangar, abin da ya fi dacewa shi ne a dare teburin sulhu wanda kuma hakan ne babbar mafita ga ma’aikatan kasar ba tare da jefa rayuwar ‘yan Nijeriya a cikin wani mawuyacin hali ba.
Ya ce, duk da rokon da gwamnatin tarayya ta yi wa NLC na ta dakatar da shiga zanga-zangar ta lumana a yau Laraba, amma mu a matsayin mu na shuwagabannin jama’a, muna tausayawa ‘yan Nijeriya halin kuncin da cire tallafin man ya jefa su a ciki.
Kazalika, “Mana sane da cewa, NLC na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana domin samarwa ma’aikata da ‘yan Nijeriya saukin rayuwa kan kalubalen da kasar ke ciki a yanzu.”
Ya kara da cewa, “Kamar sauran ‘yan Nijeriya, muna sane da cewa, ciyar da Nijeriya a gaba abu ne da ke bukatar zagewa domin a dauki matakai don amfanin kowane dan kasar, musamman da kuma yin duba ga matakan da gwamnatin tarayya ta ke kan dauka na gajeren zango domin ta saita tattalin arzikin Nijeriya.”
Ya bayyana cewa, matakan da gwamnatin tarayya tabke dauka don rage zafin radadin cire tallafin man na gajeren zango ne.
Bugu da kari, ya kuma yi kira ga shugabannin NLC da sauran kungiyoyin kwadago da suka yi hadaka da su hada hannu da majalisar wakilai a kan ci gaban da ta ke yi na tattaunawa da gwamnatin tarayya domin wanzar da shiye-shiryen da za su samar wa ‘yan Nijeriya saukin rayuwa.