Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya mika jerin sunayen ministoci kashi na biyu na shugaban kasa Bola Tinubu, ga majalisar dattawa a ranar Laraba.
Gbajabiamila ya mika jerin sunayen ne ga shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da misalin karfe 03:19 na rana bayan shigar da shi cikin majalisar.
Idan dai ba a manta ba a ranar Alhamis din da ta gabata ne Gbajabiamila ya mika jerin sunayen mutane 28 ga majalisar dattijai, inda ya yi nuni da cewa, akwai karin sunaye da za a kawo wa majalisar nan gaba kadan domin tantance su.
Talla
Cikakken labarai na nan tafe…
Talla