Sa’o’i 24 kacal bayan fara zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur a fadin kasar nan, kungiyar kwadagon ta dakatar da yajin aikin.
Shugaban Kungiyar Kwadago Festus Osifo ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a safiyar Alhamis.
- Gwamnatin Tarayya Ta Maka NLC Da TUC A Kotu Kan Shiga Zanga-Zanga
- Ƙarfin Soja Ne Matakin Da Za A Dauka A Kan Nijar -Sojojin ECOWAS
Ya ce shugabannin kungiyar tun farko sun gana da shugaban kasa Bola Tinubu sun fitar da wasu alkawura kan wasu batutuwan da aka tattauna yayin taron domin aiwatar da su cikin gaggawa.
Ya bayyana dakatar da yajin aikin ya samo asali ne a kan hakan.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa kungiyar kwadago ta Nijeriya ta bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da zanga-zanga a fadin kasar kamar yadda aka tsara tun farko, bayan wata ganawa da ta yi da gwamnatin tarayya.
Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero ya bayyana cewa sakamakon ganawar da suka yi da gwamnati bai haifar da wani sauyi ga bukatunsu ba.
Sun jaddada cewa, sun tsaya tsayin daka wajen ganin sun wakilci ma’aikatan Nijeriya da bukatunsu.