Jagoran juyin mulkin da aka yi Nijar ya yi Allah-wadai da takunkuman da ECOWAS ta sanya wa kasar, yana mai bayyana su a matsayin abin da ya sabawa doka da kuma rashin adalci.
Cikin wani sako da ya gabatarwa al’ummar kasar ta talbijin, Janar Abdoramane Tchiani, ya ce gwamnatinsa ba za ta yarda kasashen yamma ko na yankin Afirka su matsawa kasarsa lamba a kan a mayar da Bazoum kan shugabanci ba.
- Yanzu-Yanzu NLC Ta Janye Yajin Aikin Da Ta Shiga
- Ƙarfin Soja Ne Matakin Da Za A Dauka A Kan Nijar -Sojojin ECOWAS
Janar Tchiani ya kuma ce kada ‘yan kasar Faransa su ji fargabar komai.
Tuni dai Faransa ta kwashe mutane kusan 1000 ciki har da ‘yan kasarta 560, bayan da masu bore suka kai wa ofishin jakadancinta a birnin Yamai hari a ranar Lahadi.
A ranar Larabar makon da ta gabata ne sojojin fadar shugaban kasar suka hambarrar da gwamnatin shugaba Bazoum.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp