A karshen makon da ya gabata ne shugabannin Afrika suka yanke shawarar fattakar sojojin da suka hambarar da shugaban kasar Nijer Muohamed Bzaoum ta hanyar ba sojojin wa’adin mako daya na su dawo da mulkin dimokradiyya tare da dawo da shugaban kasar karagar mukinsa, ko kuma su fuskanci farmakin soja.
Shugabanin kungiyar kasashen yankin afrika ta yamma ECOWAS sun nemi sojoji su koma bariki nan da kwanaki 7 do kuma su fuskanci tsatsaurar takunkumi, haka kuma kungiyar kasashen Afrika, AU ta ba rundunar sojojin Nijer da suka hambarar da gwanatin farar hula ta Mohammed Bouzom wa’adin kwanaki 15 na su dawo da cikakken tsarin dimokradiyya a kasa Nijar ko kuma su dandana kudarsu.
- Kungiyoyin Magoya Bayan Kano Pillars Da Katsina United Sunyi Taro A Kano Domin Sulhunta Tsakanin Su
- Chelsea Ta Dauki Lesley Ugochukwu Daga Rennes
Waannan matakan da kugiyar AU da ta ECOWAS suka yanke shawarar kakabawa Nijar sun hada da kulle iyakokin kasa da na sama tsakaninta da dukkan kasashen da suke makwabtaka da ita, soke zirga-zirgar sufurin jirgin sama da kuma dakatar da harkokin kasuwanci da hada-hadar kudade tsakanin kasar da dukkkan kasashen yankin Afrika tare da kuma kwace dukkan kaddarorin kasa da ke bankuna a yankin Afrika.
Matakan da aka shirya wa masu juyin muilkin don takurasu sun hada da takunkumin tafiye-tafiye ga hafsoshin sojojin kasa tare da iyalansu. Daga karshen kuma an shirya kai musu hari don fattakarsu daga mulkin kasar ta Nijar.
Taron shugabannin kasashen yankin ECOWAS ne ta bayar da sanarwa haka a taron da suka yi a karkashin jagorancin shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu a Abuja Nijeriya.
An kuma yanke shawarar cewa, duk wata cibiya ko hukuma ta janye duk wata hulda da kasar Nijar har sai an dawo da mulkin farar hula a kasar.
Haka kuma kungiyar Ecowas ta kira taron gaggwa na shugabannin rundunonin tsaron kasashen don fito da tsari da dabarun yaki da za a yi amfani da su a kan sojojin Nijar in har sun bijire wa wa’adin da aka sanya musu.
Amma a martanin da ya bayar, shugaban sojojin da ya jagoranci hambarar da mulkin Mohammed Bazoum, Birgediya Janar Mohamed Toumba, ya bayyana cewa, taron da aka yi yana shirya kai famaki ga Nijar kuma lallai Nijar za ta kare kanta in har bukata hakan ya taso.
Tuni dai sojojin suka fara tsara yadda za su kare kan su tare da kuma neman goyon bayan al’umma kasar su, a kan haka suka nemi al’umma kasar su fito don yin zanga zangar nuna goyon bayan su ga juyin mulkin da aka yi.
Masana sun yi gargadi tare da nuna rasghin goyon bayansu ga yiyuwar daukar matakin soja da ake shiryawa, an gardadi musamman kasar Nijeriya wadda take makwabtaka da kuma iyakar kasar mafi tsawo a tsakannin sauran kasashen duniya, da kada ta sake ta yarda a auka yaki da Nijar saboda abubuwan da ka iya aukuwa da yadda rikincin zai iya dawowa ya cutar da kasa. A kan haka suka yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi hattar, kamar yadda Sanata Shehu Sani ya yi bayani a shafinsa na tuwita, ya zakulo dalilai goma sha uku da ya sa ‘yan Nijeriya ba za su goyi bayan duk wani hari da makami a Jamhuriyar Nijar ba. Duk wani hari da makami da ECOWAS za su yi wa jamhuriyar Nijar yaki ne kawai tsakanin Nijeriya da Nijar saboda kusancinmu.
Rasha da kungiyar sojojin haya na Wagner za su zo su goyi bayan Jamhuriyar Nijar, kuma Nijeriya za ta yi amfani da kudinta wajen gudanar da wannan aiki ne; da ma kuma Nijeriya ce ke bayar da kashi 70 na kasafin kudin kungiyar ECOWAS. Ba za iyi yiwu ba Majalisar Dokokin Amurka ta amince da samar da makamai marasa iyaka ga ECOWAS don yakar wata kasa ba.
Haka kuma ya kamata a fahimci cewa, jihohinmu da ke kan iyaka da suka hada da Sakkwato, Zamfara, Katsina, Jigawa da Yobe za su fuskanci hare-hare kai tsaye idan yaki ya faru. Idan babu wani matakin soji da aka dauka na fatattakar sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen Guinea, Mali, Burkina Faso da Chadi, me ya sa za a yi wa na Jamhuriyar Nijar?
Me ya sa sansanonin sojojin Amurka da na Faransa a cikin jamhuriyar Nijar suka ki dakatar da juyin mulkin, kuma yanzu suna karfafa mu mu shiga yaki?
Akwai bukatar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tuna cewa Nijar ta taimaka wa Nijeriya wajen yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda, kuma a halin yanzu kasar na karbar ‘yan gudun hijira sama da dubu 303; idan aka yi yaki tsakanin kasashen biyu wannan na iya zama cikin hadari.
Saboda haka kada shugaba Tinubu ya bari a tursasa shi ya ta da yaki da makwabciyar kasar nan, daga baya a bar shi shi kadai da yin yakin, hakan zai bar baya da kura. Babu wata kasa ta yammacin Afirka da ke da karfin soji don farawa ko ci gaba da yaki da Jamhuriyar Nijar; kowa zai dogara da Nijeriya ne.
Don haka kada mu yi kuka fiye da wadanda aka yi wa makoki; Idan al’ummar Jamhuriyar Nijar ba sa son mulkin Soja, su yi yaki su kawar da shi da kansu mana. Mu ma mun yi fada da shugabannin sojan namu, wasun mu ma sun shiga gidan yari a wannan fafutuka a baya, don haka su yi fada da nasu.
Akwai darasi mai yawa daga yanking abas ta tsakiya don har yanzu Saudiyya na ci gaba da durkushewa a Yaman bayan kashe daruruwan biliyoyin dalolin da ba mu da su.
Haka kuma Gwamnatin Myanmar har yanzu tana nan, kuma babu wata babbar kasa da take da karfi da ke tunanin daukar matakin soja.
A cikin gida Nijeriya muna famja da yaki a gida da ta’addanci, mu mai da hankali a nan, dakarun Mali, Burkina Faso da Guinea za su iya shiga yakin neman goyon bayan Jamhuriyar Nijar, kuma za su kai hari kan yankunan Nijeriya.
A kan haka dole ne Shugaba Tinubu ya ci gaba da bin hanyar tattaunawa da hukumomin soja a Nijar ba yaki ba.
Wani masanin harkokin yau da kullum mai suna, Okwy Okpala, ya ce, a halin yanzu mutane suna yin halin ko’inkula wajen kare dimokradiyya, a kan batun juyi mulkin Borkinafaso da Mali sai kuma ga na Nijar, akwai bukatar ‘yan siyasa su sake duba kawunan su da abubuwan da suke yi wa jama’a, ta yadda mutane za su yi amanna cewa, bukatunsu za su iya biya a karkashin mulkin dimokradiyya.
Lallai sojoji kwatar mulki suke yi ba zabensu ake yi ba, amma idan mutane suka tabbatar da cewa, gwamnatin dimokradiyya tana yi musu abubuwan da suka kamata su da kansu za su zage damtse wajen kare dimokradiyyar da kuma nuna wa sojoji cewa basu yarda da juyin mulki ba.
Kuma ya dace ECOWAS ta rika daukar mataki a kan duk wasu ‘yan siyasa da suka ci zabe ta hanyar magudi ba sai a kan juyin mulki kawai ba, saboda masu juyin mulki na sojoji da masu kwace zabe tamkar danjuma ne da danjummai
- Babban Kuskure Ne Nijeriya Ta Jagoranci ECOWAS Zuwa Nijar- Farfesa Dikwa
Sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi tare da kifar da gwamnatin farar hula, ta shugaban kasa Muhammad Bazoum, al’amarin da ya jawo Kungiyar Tagayyar Afrika ta ECOWAS ta yi barazanar daukar matakin soji domin dawo da gwamnatin farar hula da aka hambare, al’amarin da ya jawo zazzafan muhawara tare da fargabar abubuwan da matakin zai janyo ga al’ummar Nijeriya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, malami a Jami’ar Maiduguri, a Tsangayar Koyar da Ilimin Harsuna da Alakar kasa-da-kasa (Sociolinguistics, International Relations), Farfesa Khalifa Dikwa, ya bayyana cewa kasashen Yammacin Duniya ba abin amincewa bane kan nahiyar Afrika, musamman kasar Faransa, ya ce dole shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi kaffa-kaffa, gudun garin gyaran gira a tsone idanu.
“Abin da muke jin tsoro kar wannan rudanin ya kawo mummunan rikici tsakanin manyan kasashe, wanda hakan zai jefa Jamhuriyar Nijar shiga cikin mawuyacin halin da ko shakka babu zai shafi Nijeriya kai-tsaye. Sannan hakan zai zama karin matsala ne bisa wadda muka dade muna fama da ita a nan Nijeriya.”
“Abu na gaba kuma, idan Nijeriya ta jagoranci ECOWAS wajen fadawa Nijar; wace kasa ce a cikin Tarayyar Afrika take da wuyan daukar nauyi idan ba Nijeriya ba. Sannan kuma da irin alakar da muke da ita; tarihi, al’adu, addini da harshe sun hada Nijeriya da Nijar, ta ya za a raba mu?” In ji Farfesa Khalifa Dikwa.
Farfesa ya yi kira ga kasashen Afrika su yi karatun ta nutsu da lamarin tare da daukar darussa dangane da al’amarra da dama da suka faru a baya. Ya ce, “dole abi habyoyin sulhu da lalama wajen shawo kan al’amarin, saboda har yanzu Shugaba Mohammed Bazoum ya na hannun sojojin, (ba fata ba) idan suka kashe shi fa.”
“Idan Tarayyar Afrika ba su manta ba, a baya ma sun yi makamantan wannan barazana ga sojojin da suka yi juyin mulki a Burkina Faso, Mali da takwarorin su, amma bai yi ba. Haka zalika, ya dace Nijeriya da sauran kasashen Afrika su mayar da hankali wajen shawo kan matsaloln ta’addanci, fatara da rashin aikin yi wanda ya yi katutu ga al’umma. Wadannan matsalolin kadai sun ishemu, don Allah kar su jawo Muna wasu fitintinun.”
A hannu guda kuma ya ce babban Kuskure ne Nijeriya ta yi abin da zai bata tsakanin Nijeriya da Nijar, ya kara da cewa, “mu na tsoron makircin manyan kasashen duniya ya kaimu ya baro ta dalilin wannan matsala.”