Shugaba Bola Tinubu ya maye gurbin Maryam Shetty a matsayin minista da Dokta Mariya Mahmoud Bunkure daga jihar Kano.
Ba a bayyana dalilin da ya sa aka maye gurbin nata ba daga jerin sunayen da aka sake aike wa majalisar dattawa a ranar Laraba 2 ga watan Agusta.
- Mane Ya Jinjinawa Ronaldo Bayan Fitar Da Al Nassr Kunya
- Takaddamar Da Ta Kunno Kai Lokacin Tantance Ministocin Tinubu
Maryam Shetty, wadda ake sa ran tantancewa a ranar Juma’a, ta yi matukar kaduwa a lokacin da aka sanar da ita cewa an maye gurbinta da sunan wata.
Kamar yadda takardar da aka aike wa majalisar a ranar Juma’a 4 ga watan Agusta, 2023 da LEADERSHIP ta samu, sunanta ne na 12 daga jerin ministocin da za a tantance.
Ta isa harabar majalisar da misalin karfe 10:40 na safe domin tantance ta cike da murmushi, inda ta ke walwalwa.
Sai dai ta yi basaja tare sa barin majalisar bayan da labarin maye gurbinta ya bayyana.
Tinubu ya shaida wa majalisar dattawa cewa ta maye gurbin Shetty da Dokta Mariya Mahmoud Bunkure, tsohuwar kwamishiniyar ilimi mai zurfi ta jihar Kano a zamanin gwamnatin gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
A halin da ake ciki dai wasu ‘yan Nijeriya sun caccaki wannan mataki ja shugaba Tinubu.
Kafafen sada zumunta kuwa sun dauki dumi kan lamarin, inda wasu ke ganin ba a yi matasan Nijeriya adalci ba.