An gurfanar da wani mutum mai suna Kingsley Bassey mai ta’ammali da miyagun kwayoyi a gidan yari na Kirikiri bisa zargin kashe kaninsa a lokacin.
‘Yansanda sun kama matashin mai shekaru 23, inda aka gurfanar da shi a gaban kotun Majistare da ke Yaba karkashin jagorancin Alkali Patrick Nwaka kan zargin kisan kai.
- Sin Ba Ta Amince Da Mu’amalar Gwamnati Tsakanin Yankin Taiwan Da Amurka Ba
- Ana Ci Gaba Da Nuna Damuwa Kan Watsi Da Aikin Tashar Baro
Dansanda mai shigar da kara, Thomas Nurudeen, ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara ya aikata laifin ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023 da misalin karfe 8:30 na safe a lamba 3, a garin Meiran, Jihar Legas.
A cewar Nurudeen, laifin ya saba wa sashe na 222 kuma hukuncin da ya dace a karkashin sashe na 223 na dokar laifuka ta Jihar Legas 2015.
Laifin ya kara da cewa, “Kai Kingsley Bassey, a ranar 29 ga Mayu, 2023, da misalin karfe 8:30 na safe a lamba 3, Meiran, Legas, a gundumar Majistare ta Legas, ka kashe wani yaro dan shekara shida kisan gilla ta hanyar buga kansa a kasa sannan ya aikata laifin da ya saba wa sashe na 222 da kuma hukunci a karkashin sashe na 223 na dokar laifuka ta Jihar Legas 2015.”