Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu na girki adon mata.
Abubuwan da Uwargida za ta tanada:
Waken Soya, Kanwa, Madara Powder Flabour, Beby Mid, Sodium, Ruwa.
Da farko za ki jika waken soyar ya jiku sosai saboda gafinsa ya fita kuma ya yi haske sosai, sai ki wanke shi ki cire tsakuwar da ke ciki wato ki rege shi sai ki samu kanwa ungurno ki sa a ciki dai-dai gwargwadon yadda za ki yi misali idan na mudu daya ne sai ki sa kanwar goma ya ishe ki sai ki kai nika a nika tare da kanwar sai ki dora ruwa a wuta in ya tafasa sai ki juye kullin a cikin ruwan zafin, sai ki jujjuya shi ya hade jikinsa sai ki rufe shi amma fa ki zauna a wurin saboda bori da yake yi don kar ya zube idan ya tafasa sau biyu ko uku sai ki sauke shi ki jujjuya shi ya sha iska kadan sai ki samu abin tata ki tace shi sai ki kai shi wuri mai dumi ki rufe shi ya samu kamar awa bakwai zuwa takwas za ki ga ya yi kauri sosai, kuma kar ki cika masa ruwa a wurin tatar, sai ki samu mabirgi ki birge shi sosai ya yi sumur za ki gan shi ya yi kamar kindirmo, sannan ki zuba milk powder flabour, beby mid, sodium, amma kadan za ki sa sodium ki sa duk kayan hadin da na ambata miki.
Sai ki juya su sannan idan kina so za ki iya sa kwakwa sai ki gurza ta ki zuba yana kara masa dadi.