Shugaba Bola Tinubu ya bayyana jin dadinsa kan yadda yan wasan Super Falcons suka taka rawar gani a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA.
Inda ya kara da cewar duk da fitar da su da aka yi a bugun fanareti a zagaye na 16, ya yi matukar jinjina masu.
Tinubu, wanda ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter da safiyar Litinin bayan kammala wasan, ya ce sakamakon wasan Super Falcons ya sanya Nijeriya alfahari a fagen wasan kwallon kafa a Duniya.
“Dole ne in yaba kokarin Super Falcons a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA.
Duk da rashin nasararku kwazonku ya sa kun sanya Nijeriya alfahari a fadin Duniya”. Inji Tinubu