Kungiyar masu rajin tsaftace sana’ar POS ta Nijeriya (APOSUN), ta jaddada kudirinta na yaki da zamba da sauran haramtattun kudade da masu sana’ar na cikin mambobinta a fadin kasar nan.
Shugaban Kwamitin Amintattun Kungiyar na Kasa, Barista Ibrahim Abdullahi, shi ya bayyana hakan a lokacin da suka kai ziyarar ban girma ga wasu masu ruwa da tsaki a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Ya kara da cewa dalilin da ya sa suka kai ziyarar shi ne, domin sanar da cibiyoyin gargajiya da sauran masu hannu da shuni kan yadda za su inganta sana’arsu ta POS a Babban Birnin Tarayya da ma kasa baki daya.
Shugaban kwamitin ya kara da cewa matakin zai kuma taimaka wajen samun ci gaban tsaro tare da fadakar da mambobinsu kan shugabannin babban bankin Nijeriya (CBN).
“Ko ina aka bi a kasar nan lungu da sako za ka samu akwai mambobinmu masu gudanar da wannan sana’a ta POS, don haka ne muka lashi takobin ganin mun tsaftace sana’ar domin kaucewa yawan almundahana, zamba, damfara da sauran abubuwa na zalunci da suka addabar masu sana’ar da kuma masu zuwa domin yin mu’amala da su.
“Mun sani cewa kowace sana’a akwai mutanen kirki da kuma mutanen kawai, domin sau da yawa za ka samu wasu suna korafi kan masu gudanar da sana’ar wasu kuma masu sana’ar ne suke korafi kan masu zuwa domin mu’amala da su, in ji shi.
Don haka ya ce ya zama wajibi ga kowane mai wannan sana’a ya zama ya yi rajista domin ta haka ne za a tantance masu gaskiya da kuma marasa gaskiya, sannan kuma hakan zai taimaka wa jami’an tsaro wajen dakile haramtattun harkoki da ake yi na aika wa da kudaden fansa ga masu garkuwa da mutane.
Da yake mayar da martani kan ziyarar, Shugaban Majalisar Masarautun Abuja wanda shi ne Sarkin Abaji, Dakta Adamu Baba Yunusa ya nuna jin dadinsa ga kungiyar yadda ta bayyana su a matsayin daya daga cikin masu kokarin ganin sun tsaftace wannan sana’a ta POS, inda ya jaddada cewa za su ci gaba da mai da hankali kan yaki da zamba da almyndahana sauran haramtattun ayyuka da za su iya shafar mutucin ‘yan Nijeriya.
Sarkin na Abaji ya kuma bukaci kungiyar da ta fara horar da ‘ya’yanta domin a cewarsa hakan zai inganta kwarewarsu tare da yin gogayya da sauran masu gudanar da harkar POS a kasashen duniya.
Ya kuma yi kira gare su da su sake mai da hankali kan aikin da suka dauko domin aiki ne ja wanda dole sai sun yi tsayin daka a kansa.
“Wannan fa aki ne ja a gabanku, yanzu ya zama dole a kanku ku rika shirya taruka na wayar da kan jama’a domin wasu na shiga sana’ar ce ba tare da ilimi ba, don haka a ke ta samun korafe-korafe, ta yadda zai zama sun cuci abokin huldarsu ko shi ya cuce su, wannan duk rashin ilim ne. Don haka wannan aiki ne a gabanku na koyar da mambobinku yadda sana’ar za ta dore a samu nasara, duk abin da babu ilimi a ciknsa to lallai za a yi ta samun matsala.
“Mu kuma za mu yi abin da za mu iya na ganain mun wayar da kan jama’armu domin abin da kuka zo da shi abu ne na alheri sam barka. Ina yi muku addu’a da fatan Allah ya yi riko da hannayenku ya baku nasara,” in ji shi.
A wata ziyarar makamanciyarta da suka kai wa Daraktan Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), na Abuja, Ado Mu’azu ya tabbatar da shirinsu na yaki da zamba da almundahana, inda ya basu tabbacin goyon baya da hadin kai.
Kazalika Daraktan ya nuna farin cikinsa da samuwar wannan kungiya, inda ya ce babu shakka ya hakan zai yi tasirin sosai wajen rage zaman banza gami da sama wa matasa abin yi, sannan ya ja hankalin mambobin kungiyar da zama masu jajircewa da hakuri kan ayyukan da suka sa a gaba.
A karshe ya yaba wa shugabannin kungiyar bisa zurfin tunaninsu na samar da kungiyar, sannan kuma ya yi fatan alheri gare su da addu’ar samun nasara kan wannan ai ki da suka sa a gaba.
A halin da ake ciki kungiyar masu amfani da na’urar ta POS a Nijeriya APOSUN ta yi kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga mambobinsu a fadin jihohi domin samar da ayyukan yi da kuma ci gaban tattalin arzikin kasa.