A yau kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya yi bayani kan taron kasa da kasa game da batun Ukraine, da wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin mai kula da harkokin Turai da Asiya Li Hui ya halarci a birnin Jeddah na kasar Saudiyya a karshen makon da ya gabata.
Kakakin ya ce, an gayyaci Li Hui don halartar taron kasa da kasa kan batun Ukraine a birnin Jeddah na kasar Saudiyya, don ya yi ganawa mai zurfi da dukkan bangarorin, da yin karin haske kan matsaya da shawarwarin kasar Sin, da sauraren ra’ayoyi da shawarwarin dukkan bangarorin, da inganta yarjejeniya don warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa.
Dukkan bangarorin sun amince da kyakkyawar rawar da kasar Sin ta taka wajen inganta shawarwarin zaman lafiya. Kasar Sin za ta ci gaba da karfafa yin shawarwari da mu’amala da dukkan bangarori, da ba da gudummawa wajen sa kaimi ga warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa. (Mai fassara: Yahaya)