Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Everton, Richarlison ya koma kungiyar kwanllon kafa ta Tottenham a kan kudi flFam miliyan 60.
Richarlison, ya koma Tottenham ne bayan da kungiyoyin biyu sun bayar da sanarwar a hukumance kuma tuni aka gwada lafiyar sa ta haihuwa wato Brazil.
- Sama Da Mutum 150 Ke Hannun ‘Yan Bindiga A Jibiya – Shugaban Karamar Hukumar
- NDLEA Ta Damke Mutum 345 Bisa Safarar Kwayoyi A Jihar Katsina
Richarlison shi ne dan wasa na hudu da Tottenham ta saya bayan ta dauki Fraser Forster da Ivan Perisic da Yves Bissouma.
Har ila yau, Tottenham tana magana da Barcelona domin daukar aron dan wasan baya, Clement Lenglet dan Faransa.
Tottenham, wadda Antonio Conte yake koyarwa ta samu gurbin buga gasar cin kofin zakarun turai na Champions league a kakar wasa mai zuwa.