Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa (INEC), ta kara wa’adin kwanakin yin rijistar zabe domin bawa wadanda ba su yi ba damar yi.
A ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata ne dai wa’adin da hukumar ta bayar ya cika domin rufewa.
- Richarlison Ya Kammala Komawa Tottenham
- Hajjin Bana: Ko Hukumar Alhazan Nijeriya Za Ta Kammala Jigilar Maniyyata A Kan Kari?
Sai dai sakamakon korafe-korafe daga al’umma da masu ruwa da tsaki, hukumar ta yanke shawarar kara wa’adin ranakun kuma ta umarci ma’aikatanta a sassa daban-daban na kasar nan da su ci gaba da ayyukansu.
A wata sanarwa da Kwamishinan wayar da kan al’umma na hukumar, Festus Okoye ya fitar, ya bayyana cewa hukumar ta umarci ma’aikatanta da su ci gaba da yin rijiatar har sai an basu damar tsayawa.
“Hukumar zabe ta dukufa wajen ganin ta yi wa duk wani dan Nijeriya da ya cancanta rijiatar zabe saboda haka a shirye muke da mu cika alkawarin da muka yi” in ji Okoye.