Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika godiyarsa ga gwamnain kasar Portugal a kan yadda ta samar da dakarun sojoji a sassan Afrika don tabbatar da tsaro.
Jami’in watsa labarai na shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana haka a sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja ranar Juma’a, ya ce, shugaba Buhari, ya yi wannan jinjinar ne a taron cin abincin dare da gwamnatin ta shirya wa tawagar shugaban kasa a dakin taro na ‘National Palace Ajuda’ da ke Lisbon, babbar birnin kasar Portugal.
- Kiki-kakar Mallakar Makami A Zamfara…
- Musulman Kudu Maso Gabas Za Su Kaddamar Da Alkur’anin Da Aka Fassara Zuwa Harshen Igbo
Buhari ya kuma yaba wa shugaba Marcelo Rebelo de Sousa a kan yadda ya samar da dakaru a Afrika ta Tsakiya, inda suke gudanar da ayyukan jinkai ga kasashen Equatorial Guinea, Cape Verde da Mozambique.
Taron cin abincin ya samu halartar shugaban majalisar kasar, Augusto Santos Silva, da Frayminsita Antonio Costa da manyan jami’an gwamnatin Nijeriya da suka yi wa Buhari rakiya a ziyarar, ya kuma ce gwamnatin Nijeriya ta bada muhimmanci ga kokarin tabbatar da tsaro a yankin Afrika ta yamma.