Wani mai kula da sashen cinikayya na duniya na ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin ya bayyana a yau cewa, kasar Amurka, a matsayinta na kasa mai mafi girman tattalin arziki a duniya, kuma babbar kasar da ta kafa da kuma cin gajiyar tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban, ta yi watsi da ka’idoji da alhakinta a shekarun nan, ta aiwatar da cin zarafi na cinikayyar bai daya, da yin munafurci a manufofin masana’antu, da kawo cikas ga yadda masana’antu ke samar da kayayyaki a duniya, da kin aiwatar da hukuncin WTO, da yin mummunar illa ga aiwatar da gyare-gyare da ci gaban kungiyar WTO. Kasar Sin ta yi kira ga Amurka da ta gaggauta gyara munanan kalamai da ayyukanta, da kuma bin ka’idojin WTO yadda ya kamata da cika alkawurran da ta dauka.
A yau, ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta fitar da “Rahoto kan aiwatar da ka’idoji da takalifi ta WTO daga Amurka”, inda ta takaita bayyani kan yadda Amurka ta bi ka’idoji da takalifin WTO, tare da yin cikakken nazari, da nuna damuwa kan manufofi da matakan Amurka kamar tarwatsa tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban da aiwatar da cin zarafi na kasuwanci bai daya. (Mai fassara: Yahaya)