Biyo bayan gaza shawo kan yajin aikin da kungiyar Malaman jami’o’i suka tsunduma (ASUU), kungiyar Kwadago a Nijeriya (NLC), ta umarci mambobinta da su yi zaman shirin gudanar da jeren gwanon zanga-zanga a duk fadin kasar nan.
Zanga-zangar wacce za su gudanar domin nuna goyon bayan ASUU a kan kokarin da take yi na ganin an cimma bukatun da malamai suke da su domin kyautata jami’o’in kasar nan.
Shugaban NLC na kasa, Comrade Ayuba Wabba, wanda ke magana a lokacin ganawa da Majalisar koli na kungiyar a Abuja, ya kuma nuna damuwarsu bisa korar malamai da Gwamnatin jihar Kaduna ta yi a kwanakin baya.
Kwamared Ayuba ya kara da cewa, jihohin Zamfara, Abiya, Taraba da Kuros Riba har yanzu ba su fara aiwatar da sabon tsarin biyan albashi mafi karanci na dubu 30 ba.
Kazalika, kungiyar ta kuma yi kira ga shugaban ma’aikata na gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan, da su wallafa sunayen mutanen da suka ayyana a matsayin ma’aikatan bogi su 70,000 da tsarin IPPIS ya bankado.