Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa da ku a wannan mako a cikin shirin na mu na Girki Adon Mata, inda yau za mu yi magana a kan yyada ake hada Miyar Ridi.
Ga dai abubuwan da uwargida za ki tanada;
Ridi, Kifi busasshe, Nama, Tattasai da Attaruhu da Tumatur Albasa, Magi, Gishiri, Kuri, Ugu.
Yadda Uwargida za ki hada:
Da farko ki wanke Ridinki wadatacce ki shanya ya bushe
Sai ki raba biyu, ki nika rabi, ki soya rabi, ki soya shi har sai ya fara kamshi amma kar ki barshi ya kone ya yi baki sai ki sauke.
Sai ki kawo kayan miyarki wanda dama kin gyara su, sannan kuma kin malkada su masu dan yawa saboda tana son kayan miya mai dan yawa ki sa nama idan kin samu naman rago ya fi dadi sai dai idan baki samu ba da gyararren kifinki busasshe ki soya su tare da kayan miyanki, kada su soyu so sai.
Sai ki tsaida ruwa ki rufe.
Idan ya tafasa ya yi kauri sosai sai ki kawo nikakken Ridinki ki zuba ki sa maggi da kuri da gishiri da sauran kayan kamshi duk wanda kike da shi za ki iya zubawa sai ki rufe kibarshi ya yi kamar minti 10 haka,
Sannan sai ki kawo yankakken Ugu, kananan yanka, da ‘yan kakkiyar albasa sai ki zuba, ki kawo Ridin ki soyayye wanda baki nika ba ki zuba ki jujjuya sai ki rufe, bayan minti biyar sai ki sauke.
Za a iya ci da tuwon shinkafa, Sakwara, Sinasir ko masa, da funkaso.